Tawagar masu bincike na kasar Sin ta yi nasarar samar da ingantacciyar fasahar rabe tsakanin hanyoyin da ke aiki da ma’aunan sinadarai da gangar jiki na batirin lithium tare da wallafa sakamakon binciken nasu a mujallar ilimi ta Nature.
Wannan fasaha ta rabe hanyoyin ta kunshi babbar garkuwar hana hadewar hanyoyin lantarki, da habaka saurin aikin sinadaran caji da daidaita amfanin sauran sinadaran, ta yadda za a samu ingancin aiki da amincin amfani da batirin na lithium, kamar yadda shugaban tawagar binciken, Yan Keyou na jami’ar fasaha ta kudancin kasar Sin ya bayyana.
Ana sa rai wannan nasara da aka samu ta bayar da sabbin fasahohi na kimiyya masu muhimmanci domin bunkasa ci gaba da kuma kera baturan lithium masu ingancin aiki. Kazalika, ana iya amfani da fasahar wajen habaka ci gaba a fannoni kamar na kera motoci masu aiki da sabbin makamashi, da samar da hadaddun fallayen zuko makamashin hasken rana, da sarrafa shi zuwa lantarki tare da adana shi. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)