A yau Alhamis aka gudanar da wani taron ƙara wa juna sani a Cibiyar Al’adun Kasar Sin da ke Babban Birnin Tarayya Abuja mai taken “Gyare-gyaren kasar Sin a Sabon Zamani”.
Taron wanda aka gudanar bisa hadin gwiwar cibiyar al’adun da Hukumar Kafofin Watsa Labarai ta Kasar Sin (CMG) ta samu halartar kwararru da manyan baki wadanda suka yi karin haske a kan gyare-gyaren da kasar Sin ta tsunduma yi da kuma alfanunsu ga al’ummar duniya.
An fara taron ne da gabatar da jawabin Mataimakin Daraktan Sashen Yada Labarai na Kwamitin Tsakiya na Jam’iyyar CPC kuma Darakta Janar na Hukumar Kafofin Watsa Labarai ta Kasar Sin, Mista Shen, inda ya nuna muhimmancin dorewar hadin gwiwa tare da mika godiya ga mahalarta taron.
Mista Shen, ya jaddada wajibcin hadin kai a tsakanin al’ummomin duniya domin cimma muradun ci gaba da kowa da kowa ke hankoron gani.
Har ila yau, masu gabatar da jawabai daban-daban a wurin taron sun yi gamsassun bayanai game da rawar da kasar Sin ke takawa wajen taimaka wa ci gaban kasashen duniya.
Musamman wacce ta yi fashin baki a kan tasirin da kasar Sin ke yi wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, Fa’iza Muhammed, ta ce ba karamar gudunmawa kasar Sin ta bayar wajen daidaita turbar habakar tattalin arzikin Nijeriya ba.
A nata bangaren, wakiliyar Ministar Bunkasa Yawon Bude, Misis Patricia Naria, ta mayar da hankali ne a kan yadda za a ciyar da harkokin yawon bude ido gaba a Nijeriya, kana ta nemi a karfafa matasa domin takaita kwararar mutane daga kauyuka zuwa birane.
Shi kuwa, Mista Raphael Oni, ya yi bayani ne a kan abubuwan da za a iya cimmawa idan aka samu hadin gwiwa da inganta kwazon aiki tsakanin kasashen duniya, kana ya yi tsokaci a kan irin rawar da Sin ke takawa wajen samar da ma’aikata a sassa daban-daban na ci gaban Nijeriya.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Nijeriya Da Suka Samu Horo a Kasar Sin, Malam Mohammed Sulaiman, ya yi karin haske a kan muradun ci gaban kasa da Sin ta sanya a gaba da kuma kokarin da take yi na zamanantar da harkokinta tare da tabbatar da dorewar bunkasar duniya da zurfafa ci gaban kimiyya.
Daga bangaren Mista Okon Emmanuel kuwa, ya nuna muhimmancin shigar da matasa ne cikin harkokin yawon bude ido domin a dama da su, yayin da ita kuma Edi-ima Ekpety ta yi bayyana abubuwa masu ban sha’awa da ta koya a kasar Sin lokacin da take karatu a can inda ta nuna alfanun sanin al’adun juna da kuma damammakin karo ilimi da ake samu.
An dai kammala taron ne da jawabin mai gabatar da taron wanda ya nuna muhimmancin abubuwan da baki masu gabatar da jawabai suka bayyana tare da daukar hotuna da ke nuna sabunta hadin kai da zumunci a tsakanin mahalarta taron.
Za a iya cewa taron na kara wa juna sani da aka gabatar, ya samar da wata kafa ta tattaunawa da musanyar ra’ayoyi da kuma Karin haske a kan manufar gyare-gyaren da Sin ke yi da yadda abin zai amfanar da duniya tare da jaddada muhimmancin hadin gwiwa a tsakanin Nijeriya da Sin domin a gudu tare a tsira tare.