Wani masani a bangaren ilimin abinci, Dakta Olugbenga Bankole, ya shawarci mata masu aikin gwamnati da su tabbatar da aikinsu bai kawo musu cikas ba wajen shayar da jariransu nono a dukkan lokaci don tabbatar da lafiyar jariran nasu.
Dakta Bankole, wanda jami’i ne a hukumar lafiya ta Jihar Kwara, ya bayar da shawarar ne a tattaunawarsa da manema labarai ranar Alhamis a yayin bikin ranar shayar da jarirai nonon uwa na wannan shekarar ta 2022.
- Yadda Ridi Da Kwai Ke Gyara Jikin Mace (2)
- Ministar Jin Kai Ta Raba Wa Mata 3,500 Tallafin Kudi A Gombe
An ware watan Agusta na kowacce shekara don fadakar da al’uma a kan muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa tare da kuma karfafa wa hukumomin gwamnati don su samar da yanayin da mata masu aiki za su samu lokacin da zasu ba jariransu nono ba tare da matsala ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp