Masana harkokin kiwon lafiya, sun gargadi ‘yan Nijeriya kan yin amfani da wasu kayayyakin masarufi, wadanda a hukumance ba a bayar da izinin yin amfani da su ba, ciki har da wani sinadari gishiri, wanda a yanzu haka yana iya cutar da lafiyar Dan Adam, sakamakon illar da ke tattare da shi kamar yadda Royal Ibeh ya bayyana.
Har ila yau, masana harkokin kiwon lafiyar da kwararru a kan harkar sarrafa abinci, sun yi wannan gargadi tare da jan hankulan ‘yan Nijeriya, da su zama masu lura a kan ire-iren abincin da za su kai kofar bakunansu.
- Dan Majalisa Zai Aurar Da Mata Marayu 100 A Kebbi
- Zaben Kano: ‘Yansanda Da Masu Zanga-zanga Sun Yi Arangama A Kano
A ‘yan kwanakin nan ne, aka samu a wasu yankunan Arewacin Nijeriya, an kai wani sinadarin gishiri; wanda a hukumance babu izinin yin amfani da ana sayarwa, inda ba tare da wani bata lokaci ba; masana suka bayar da sanarwar cewa, ba mai inganci ba ne; zai kuma iya cutarwa.
“Wannan wani sinadarin gishiri ne, mai karfin gaske da aka jima ana amfani da shi shekara da shekaru, don kara dandano da kawata girkin abinci.
Wani kwararre a kan harkar sarrafa abinci, Isah Kareem ya bayyana cewa, wajibi ne mutane su lura da irin sinadaren kayan abincin da suke amfani da su a gargajiyance, don kara dandanon abincinsu na yau da kullum, domin kauce wa fada wa hadarin cutar da lafiyarsu.
Ya kara da cewa, “duk dadin da abinci zai yi idan aka yi amfani da ire-iren wadannan abubuwan da hukuma ba ta bayar da izinin yin amfani da su ba, a bar su ya fi alhairi domin kuwa ko shakka babu akwai hadari a tattare da su.
Sannan, ire-iren wannan gishiri, ana sayar da shi a bude ba kamar irin sauran kayan kamfani da ake adana su da kyau ba, duk da dai masu saye na rububunsa ne; saboda ganin garabasa ko arha, wanda kuma ita arha kamar yadda masu iya magana ke fada, ba ta ado.
Haka zalika, sinadarin gishirin da Hukumar NAFDAC ta amince a yi amfani da su sun hada da; Ajinomoto, Beda da sauran makamantansu, wadanda suke a cikin sacet na leda a killace ake sayar da su. Amma wadannan; wadanda ba a cikin sacet na leda suke ba, kai tsaye sun sha ban-ban da wancan.
Don haka, babu ta yadda za a iya gane alama ko wata sheda ta kamfani, ballantana a iya tabbatar da ingancinsa. Kari a kan hakan shi ne, ana sayar da shi da matukar arha; wanda duk mai hankali zai iya tabbatar da cewa, lallai wannan ba abu ne mai inganci ba, sannan kai tsaye zai iya cutarwa”.
Wata masaniya harkokin kiwon lafiyar, Foloke Ojo ta bayyana yadda a kullum ta duniya, ake kai ire-iren wadannan kayan amfanin abinci ake sayarwa, shi kuma mai saye babu abin da ke gabansa, illa dandanon da zai samu da kuma arhar abin sayarwar. Sannan, wasu ma amfani suke yi da sunayen wasu kamfanonin tare da ikirarin cewa, hajar tasu ta fi kowace haja kyau da inganci.
Ta kara da cewa, “kai ire-iren wadannan kaya tare da sayar da su a kasuwanni, ya jima da zama ruwan dare. Duk da cewa, Hukumar NAFDAC da ta SON, na bibiyar kasuwannin suna bincikawa, don bankado kayan jabu da wadanda hukuma ba ta bayar da izinin sayar da su ba”, in ji ta.