A ranar Lahadin da ta gabata, 28/6/2022 masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta yi babban rashi, inda aka wayi gari da alhinin rashin tsohon Jarumi kuma babban Daraktan da ya dade yana ba da gudunmawa cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wanda a kalla zai kai kimanin shekaru 25 a cikin masana’antar.
Jarumin wanda shi ne babban daraktan shirin nan mai dogon zango na ‘Izzar So’ wato NURA MUSTAPHA WAYE.
Shi dai dan asalin garin Kano ne, wanda ke zaune a unguwar Goron Dutse, ya rasu yana da shekaru 43, ya bar matarsa guda daya da kuma yara sha daya, Wakiliyar mu RABI’AT SIDI BALA ta ji ta bakin wasu daga cikin manyan abokan sana’arsa da ke zaune a wajen zaman makokin ta’aziyyarsa, inda suka bayyana wasu abubuwa da jama’a ba su sani ba sosai game da shi, da kuma irin kudurin da yake dauke da shi tun a farkon zuwansa cikin masana’antar ta Kannywood, har ma da wasu batutuwan na daban. Ga dai bayanan na su kamar haka:
Sunana Lawan Ahmad:
Assalamu Alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu. Shi dai wannan bawan Allah, halayensa wanda jama’a ba su sani ba na alkhairi, kusan na ce jama’a sun sani. Farko shi ne kaunar Manzo (SAW), kuma duniya ta riga ta san haka. Sannan mutum ne da ba za a taba ganin sa ya na fada da wani ba, sannan mutum ne mai son duk inda ya ji ana abu wanda ba dai-dai ba ko da za a yi fada da shi wallahi sai ya san yadda ya yi ya hana, sai dai in daina kula shi za a yi a daina, amma sai ya fadi gaskiya.
Ba shi da wani aiki illah ya ga cewa kowaye mutum ya tsare hakkin Manzon Allah (S.A.W), ya tsare hakkin ubangiji, abin da Allah ya fada da Allah ya ce a yi, da wanda Allah ya hana shi ne burin Nura ya ga ya samar da shi a ko ina, a duk inda yake kuma kowaye, komai girmanka, komai kudinka, in mace ce komai kyanki, komai kudinki, zai fada miki gaskiyar al’amari a kiyaye hakkin Allah, sannan abin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya fada.
Bugu da kari, Nura idan ya ga wani da wani suna fada to sai ya san yadda zai yi ya shirya su, ko ma ya ya ne, duk yadda zai yi ya shirya su ina tabbatar miki da cewa sai ya shirya su, in takaice miki Nura bai da wata matsala a rayuwa.
Wallahi ba wata rashin lafiya da ya yi a kwana hudu da suka wuce ne ni ne na yi rashin lafiyar ‘Ulcer’ ta ta tashi na je asibiti aka yi min allurai aka ban magani, sai washegari ne nake bashi labarin abin da ya faru, sai yake fada min shi ma jikinsa ya dan dame shi amma ya warware. Wannan maganar ita muka yi kuma washegari muka fita aiki, ranar Asabar muka tafi aiki har karfe 10 na dare muna aiki, muka tashi muka tafi wurin ‘Editing’ na fim dinmu muna ‘editing’ a can na bar shi na tafi tun da za mu saki Izzar So na ranar Lahadi, sai ya gama jera wa ya yi ‘editing’ sannan za mu cire shi washegari Lahadi za mu dora shi, to! washegarin Lahadi shi ne Allah ya karbi rayuwarsa wurin karfe bakwai da rabi aka kira wo ni kafin takwas, kuma yana karatun alkur’ani, ‘yan unguwar ma cewa su ka yi ana bude masallaci da Asubha shi ya fara shiga.
Lokacin da aka sanar mun ya rasu ban yarda ba gaskiya, lokacin ma ina hanyar Katsina aka gaya mun na ce wannan wace irin magana ce ake gaya min bayan jiya mun rabu da shi lafiya, sai aka ce min dai na zo an kai shi Asibiti kafin na zo an dawo da shi gida, amma da na zo kan gawarsa ni maganar gaskiya ban yarda ya mutu ba, sai na ce sai an kara kirawo likita ya kara duba shi, da aka kira likita ya zo ya kara duba shi ya kara tabbatar min da cewa babu rai a jikin Nura, shi ne dai na yarda cewa Nura Allah ya karbi abinsa, kuma daman ita mutuwa da rayuwa duk na ubangiji ne, sannan babu tsumi babu dabara ba mu san abin da Allah zai yi da bawansa ba, tun da shi ya halicce shi mu ma duk jira muke Allah’n ya yi iko akan mu ya yi yadda ya ga dama.
Nura ya yi wasu fina-finai amma ba wanda ya yi fuce kamar Izzar So, ya dade yana yin aiki amma da yake labarin da yake ba irin wanda ya jibanci irin na Izzar So din bane ba, amma ya dade a masana’antar gaskiya, zai kai kamar shekara Ishirin da wani abu.”
Adam M. Adam:
Salamu alaikum warahmatullahi ta’ala wa barakatuhu, Sunana Adam M. Adam daya daga cikin Jarumai na masana’antar Kannywood. Wallahi wannan mutuwar ta daga wa kowa hankali ba ma mu da muke cikin masana’antar fim ba, har na wajen masana’antar fim din ma wadanda suke bibiyar ayyukan mu idan mun yi sun shiga cikin tashin hankali, kuma Nura Mustapha Waye duk wanda ya san shi, in dai ya taba ganinsa ko sun taba mu’amula, to zai gaya ma wane ne Nura Mustapha Waye.
Saboda na farko shi dai ba shi da abokin fada, ba shi da abokin da za a ce wannan suna gaba da shi ko wani ka za, kullum kiransa ga mutane a so juna, a bi Allah, a bi Manzon Allah (S.A.W), shi ne burinsa a cikin rayuwarsa. Kuma Nura Mustapha Waye tun kan ma in zo a wannan lokaci da Allah ya kawo masa daukaka yake da wani zil a cikin zuciyarsa ko kuma yana da wani kuduri da shi yake so ya canja irin fina-finan da ake yi a masana’antar fim, wanda za ki ga yawancin wasu fina-finan da ake yi za ki ga kawai fim ne da aka yi shi babu wani muhimmin sako babu da aka tura ga addini, babu wasu abubuwa da yawa tun da kin san kowa da yanayinsa.
To, shi kuma babban burinsa a duniya Nura Waye mutum ne wanda yake son Annabi, duk maganar Nura Waye daya biyu a duniya za ki ji ya ce Annabi ko Allah ya sa Annabi ya yi mana ka za, ko Allah ya sa Annabi ya cece mu, kullum maganarsa kenan. Kuma Allah cikin ikonsa da ya kawo wa Nura Waye daukaka a cikin wannan fim da muke yi na shirin Izzar so wanda silar fim din fim din Lawan Ahmad ne, da shi kansa Lawan Ahmad din da Nura Mustapha Waye din da duk sauran Jaruman da suke fito wa a cikin fim din babu wanda bai samu karbuwa ba ko daukaka a cikin fim din ba.
Sannan abin da ya kara daukaka fim din wallahi maganar Annabi ko kuma zila sakon Annabi a ciki jama’ar duniya har suka gane waye Nura Mustapha Waye. Idan za a saki ‘Episode’ duk Lahadi muke saki da wahala ka kalli ‘Episode’ din nan farko zuwa karshe ba ka ga sakon Annabi a ciki ba, kuma dama babban burinsa kenan, kuma Nura Mustapha Waye burinsa ya cika kuma ya tura sakon Annabi, kuma ya tafi kuma jama’a sun karba, sannan sun yarda da Nura Mustapha Waye mutum ne me son Annabi.
Kazalika duk mutumin da ya zo ya ga mutuwar Nura Mustapha Waye ya san Annabi ya yarda da shi, kuma mutuwarsa ko mu yanzu da muke cikin doron duniya ni na roki Allah madaukakin sarki kai min arziki da mutuwa irin ta Nura Mustapha Waye, ko kuma makamancin irinta. Ya tashi an yi Sallar Asubha da shi ya riga limamin ma zuwa masallaci, ya fito ya je ya yi lazumi ya yi karatun Alkur’ani, ya dauki dansa ya kai shi makaranta, sannan ya shi ga gida.
Ya shiga gida da littafai a hannunsa ya shiga gun mahaifiyarsa ya ce “Hajjiya ina neman ki yi mun gafara”, sai ta ce “Me ka yi mun, sai ya ce “Babu komai ni dai kawai ki yi min gafara”, ta ce “Ni wallahi ba ka yi min komai ba, ya shiga cikin dakinsa ya shiga cikin dakinsa an dafa masa ruwa shayi zai sha to, akwai wata ‘yar uwa ce gare shi ina jin sai suka dan samu matsala da mijinta sai ya daga waya yana ma ta waya, yana ce ma ta “Ki bi aure ki bi mijinki, aure rayuwa ce ta addini, ta ka za da ka za, ya na yi ma ta fada yana cikin yin wannan fadan waya ta fadi daga hannunsa kawai ya kifa.
Tun da Nura Mustapha waye ya yi wannan kifawar bai farka ba sai a alkiyama, Allah ya zare rayuwarsa babu doke-doke, babu ihu, babu tashin hankali, in ka zo ka ga Nura Mustapha Waye duk mutumin da ya ganshi wallahi-wallahi zai dauka bacci yake yi.
Sunana Shu’aibu Idris (Lilisco), Mataimakin shugaba na Hausa Actors Clubs of Nigeria:
Da farko dai gaskiya mun yi babban rashi, domin rashi ne da zan ce ya taba kowa a cikin masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood. Nura Mustapha Waye a baya kamar shekara 25 jarumi ne kuma Darakta, yana fito wa a cikin fina-finai, daga baya ya haura ya daina fita ya koma ba da umarni.
Nura mutum ne wanda ya zauna lafiya da al’umma, ba za ka ga abokin fadansa ba, kuma mutum ne da yake da son addini, kuma mutum ne wanda a dukkanin fina-finan da ya fara tun fil azal da na san Nura, tun yana zuwa muna zama da shi a ofis dina duk abin da zai yi sai ya yi kokarin cusa addini ko yaya ne a cikin sana’arsa don ya nuna mahimmancin addini da kuma al’ada.
Mutum ne da ya samu yabo ta ko ina, ta ko wanne bangare don haka mu a wajen mu ba karamin rashi ne wanda ba za mu manta da shi ba, domin ya ba da gudunmawa dari bisa dari a cikin wannan masana’anta, don a takaice ya samu kusan shekaru 25 a cikin wannan masana’anta zuwa 24. Ni na yi masa tsohon sani ba tun yanzu ba, wasu ne za su ga kamar a Izzar so kawai ya fara daraktin ya yi suna, amma tsohon Jarumi ne kuma tsohon Darakta ne ya dade a cikin masana’antar, rashin wannan bawan Allah da muka yi, kuma kafin a sami wanda zai cike gurbinsa gaskiya za a dan juma.
Sabida kokarin da yake ba wai kawai iya ba da umarni ba ne, yana kokari ya ga ya hidimtawa addini dai-dai gwargwado ya shigo da wani abu wanda zai fadakar da mutane ko kuma ya sanar da mutum ko kuma ya dora mutane akan wannan kadamin mahimmancin ka rike addininka.
Don haka mu babban rashi ne a wurinmu gaskiya babu abin da za mu ce sai dai Allah ya ji kansa, Allah ya gafarta masa, Allah ya kai Rahma kabarinsa, ‘Ya’yansa da ya bari da matansa ubangiji Allah rika musu, mu kuma ‘yan uwansa da abokan arziki Allah ya kara ba mu hakuri.
Fim dinsa na farko sunansa ‘Waye’ a nan ya samu sunan Nura Mustapha Waye, ya yi fim a kalla zai kai kamar guda 250.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa idan Allah ya kai mu.