Bisa gayyatar Luiz Inácio Lula da Silva, shugaban Jamhuriyar Tarayyar Brazil, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 a birnin Rio de Janeiro tare da yin ziyarar aiki a kasar ta Brazil daga ranar 17 zuwa 21 ta Nuwambar da muke ciki.
Masanan yankin Afirka sun bayyana cewa sun-kasa-sun-tsare suna sauraron muhimman shawarwarin da Shugaba Xi zai gabatar, kana suka yi fatan kasar Sin za ta ba da gudunmawar karin hikimomi da karfinta wajen inganta shugabanci a duniya, da habaka dorewar ci gaba da kuma aiki tare da kasashe masu tasowa domin cimma nasarar murmurewarsu.
- Jarin Da Ake Zubawa A Fannin Bincike Da Samar Da Ci Gaban Manyan Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Haura Yuan Tiriliyan 1
- Jimillar Darajar Kwangilolin Da Aka Daddale Yayin Baje Kolin CIIE Karo Na 7 Ta Zarce Dalar Amurka Biliyan 80
A tsokacin da ya yi, wani kwararre mai fashin baki a kan tattalin arziki da siyasa a kasar Ruwanda Dr. Rusa Bagirishya, ya nunar da cewa, a lokuta da dama Xi ya jaddada batun ‘yancin ciniki, da samar da ci gaban da ya hade kowa da kuma cimma nasarar moriyar juna a taron koli na G20 wanda tabbas, wannan ya yi dai-dai da kiraye-kirayen samun dorewar ci gaba da ake yi a duniyar yau.
Idan za a iya tunawa dai, a watan Satumbar da ya gabata, an gayyato Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta zamo cikakkiyar mamba a Kungiyar G20. A nashi bangaren, Dr. Balew Demissie, farfesa a Jami’ar Addis Ababa ta kasar Habasha, ya bayyana cewa kasar Sin ita ce kasa ta farko da ta nuna goyon bayan shigar kungiyar AU cikin kungiyar G20, inda hakan ya taimaka gaya wajen bai wa Afirka karin damar fada-a-ji a batun shugabanci na duniya.
Kasashen Afirka suna fatan ziyarar Shugaba Xi za ta kara taimakawa da hikimomi na fadada fada-a-ji da da samun wakilcin kasashe masu tasowa da kuma taimaka wa daidaita tsarin shugabanci na duniya mai adalci da ciyar da kowa gaba.