Wani masani dan kasar Zimbabwe ya bayyana a jiya Laraba cewa, ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ke yi yanzu haka a Afirka wata alama ce dake nuna yadda zumunci mai karfi ya dade da kulluwa a tsakaninsu.
Masanin, wanda yake babban darakta a cibiyar nazari da bincike kan al’amuran kudancin Afirka da ta kasance babban rukuni na gudanar da binciken yanki, ya kara da cewa, shekaru 35 ke nan a jere da ministocin harkokin wajen kasar Sin suke zabar Afirka a matsayin yankin da za su fara kai ziyara a kasashen waje, wadda hakan na nuna yadda Sin ke bin manufofinta ba tare da yankewa ba da kuma fayyace Afirka a matsayin babbar kawa.
- Xi Ya Jagoranci Taron Shugabannin JKS Game Da Ayyukan Tallafin Jin Kai Bayan Aukuwar Girgizar Kasa A Xizang
- Tsakanin Sin Da Afirka: Zumunta A Kafa Take
Madakufamba ya ce, a matsayin babbar kawar cinikayyar Afirka tsawon shekaru 15 a jere, kasar Sin ta ci gaba da kara yawan kasuwancin da take yi da yankin har abin ya kai dalar Amurka biliyan 282.1 a shekarar 2023.
Ya kuma ce a kwanan baya, kasar Sin ta fara aiki da manufar soke haraji baki daya a kan kayayyakin da ake shigo da su kasarta daga kasashen Afirka 33 marasa karfin tattalin arziki, inda hakan yake bunkasa cinikayya da Afirka da kuma kara yawan damammakin kasuwanci a Afirka.
Madakufamba ya jaddada cewa, muradun kasar Sin a Afirka na cin moriyar juna ne da ke bai wa ko wane bangare damar cin gajiyar kawancen da ake yi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)