Masarautar Bauchi ta janye matakin da ta É—auka na soke Hawan Daushe, inda yanzu ta tabbatar da cewa za a gudanar da bikin kamar yadda aka saba kowace shekara.
A baya dai masarautar ta nemi a É—age hawan na bana, kuma Gwamna Bala Muhammad ya amince da hakan.
- Chelle Ya Fara Da Ƙafar Dama A Super EaglesÂ
- Ranar Mata Ta Duniya: NPA Ta Mayar Da Hankali Wajen Kare ‘Yancin Mata –Dantsoho
Sai dai, bayan ‘yan sa’o’i, masarautar ta sauya matsaya, inda ta sanar da cewa za a gudanar da Hawan Daushe kamar yadda aka saba.
Magatakardan Majalisar Masarautar Bauchi, Alhaji Shehu Mudi Muhammad, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki, an cimma matsayar ci gaba da bikin.
“Masarautar Bauchi tana farin cikin sanar da jama’a cewa za a gudanar da Hawan Sallah na 2025 kamar yadda aka tsara.
“Bayan nazari da tattaunawa da gwamnati, Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya amince da gudanar da wannan gagarumin biki,” in ji shi.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a fitar da cikakken jadawalin shirye-shiryen hawan nan gaba kaɗan, tare da fatan Allah Ya sanya ayi bikin lafiya.
A tarihi, Hawan Daushe yana da muhimmanci sosai a al’adun Bauchi, inda sarakuna da masu riÆ™e da mukamai ke hawa dawakai cikin shiga ta alfarma, tare da nuni da al’adun gargajiya.
Hakan yana jan hankalin jama’a da yawon buÉ—e ido daga sassa daban-daban.
Masarautar Bauchi ta jaddada cewa ba a bayyana haƙiƙanin labari ba, kuma kwamitin da ke kula da hawan ne ya nemi a soke bikin da farko.
Sai dai bayan shawarwari, yanzu an tabbatar da cewa za a yi Hawan Daushe kamar yadda aka saba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp