Masarautar Gwandu a Jihar Kebbi ta sanar da shirye-shiryen farfado da hawan doki na gargajiya da ake gudanarwa a duk shekara, a wani mataki na ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’ummarta.
Babban mai kula da kwamitin hawan Alhaji Mustapha Usman-Adamu, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Birnin Kebbi. An tsara gudanar da taron a watan Nuwamba na shekarar 2024.
- WATA SABUWA: Ganduje Ya Nuna Rashin Jin Daɗi Bayan Tinubu Ya Masa Tayin Muƙamin Jakada
- Na Amso Sakon Sirri Ne Daga Buhari Zuwa Ga Bagudu Da Sarkin Gwandu – Farfesa Gambari
Usman-Adamu, wanda ke riƙe da sarautar Sarkin Bargun Ka’oje, ya bayyana cewa wannan yunƙuri na da nufin haɗa kan mutane daga sassa daban-daban na gundumar Gwandu, wadda ke ɗauke da ƙananan hukumomi 10 da shugabannin gundumomi 55. Ya ƙara da cewa wannan yawan Sallah, wanda addinin Musulunci ya yarda da shi, zai taimaka wajen gyara alaƙa, da ƙarfafa zumunta a tsakanin dangin sarauta, tare da bunƙasa tattalin arziƙin yankin.