Masarautar Katagum tana cikin Jihar Bauchi a Tarayyar Nijeriya ne, kuma daya ce cikin masarautun da suka karbo tuta daga Shehu Usman Danfodiyo.
Masarautar a yanzu ta tashi ne daga garin Katagum in da canne ainihin tushen ta, lokacin da almajirin Shehu Usman Danfodiyo wato Malam Ibrahim Zaki ya karbo tuta ya kuma kafa masarautar,sai dai a halin da ake cikin yanzu ta dawo cikin garin Azare.
Sai dai har yanzu tana amsa sunanta na Katagum,ko da yake shi garin Katagum Hakimi ne yake iko da shi, wato Galadiman Katagum.Kuma Katagum shi ne ke zaman hedikwatar karamar hu kumar Zaki a jihar Bauchi. Sarkin Katagum da ke kan karaga shi ne Alhaji Umar Farouk, wanda ya gaji Sarkin Katagum Alhaji Dakta Muhammadu Kabir Umar CON.(1980-2017)
Azare
Azare birni ne, da ke a jihar Bauchi, a tarayyar Nijeriya.Malam Zaki ne ya kafa shi wanda kuma Shehu Usman Danfodio ya nada shi a farkon shekarar 1814.Azare hedikwatar Katagum ce a jihar Bauchi, garin Azare yana da iyaka ne daga gabas da karamar Hukumar Damban da Potiskum jihar Yobe, daga kudu kuma karamar Hukumar Misau ce,yayin da daga yamma kuma karamar Hukumar Jama’are, daga Arewa kuma ta yi iyaka da karamar hukumar Gadau a Jihar Bauchi.
An kafa garin Azare ne a shekara ta 1803 kimanin Shekaru (219) kamar yadda aka samu bayani daga iyalan Malam Lawan, mahaifin Sarakunan farko da na biyu na Azare. Malam Bonni ya kasance kanin Malam Zaki.Malam Ibrahim Zaki shi ne mazaunin garin Azare na farko, dan Malam Lawan ne wanda ya rasu a kauyen Yayu da ke kusa da Chinade.
Malam Lawan ya fara zama a garin Nafada dake cikin masarautar Gombe wanda daga baya kuma ya koma garin Yayu inda ya haifi dansa Zaki.
Bayan rasuwar Malam Lawan, Malam Zaki ya je wurin Sheikh Usman Danfodio da ke Sakkwato domin ya karbi ragamar mulki a madadin Malam Lawan.
A shekarar 1814, Malam Zaki ya kammala makarantar Islamiyya ta Sheikh Usman Dan Fodio da ke Sakkwato, a wajen shekara ta 1809,ya fara zama a kauyen Tashena mai tazarar kilomita 9 daga Azare ta yanzu, Malam Zaki ya fara mulki ne daga 1807 zuwa 1914, sai kuma dan’uwansa ya gaje shi, wanda aka fi sani da Sulaiman Adandaya daga shekarar 1814 zuwa 1816.
Kamar yadda tarihi ya nuna, Sarkin Katagum na uku shi ne Malam Dankauwa wanda ake kallonsa a matsayin mutum mai karfin gaske. Yana da mahayan dawakai kimanin 4000 da sojoji masu kafa 20000 wadanda ya yi yaki da su da yawa kuma ya yi sarauta tsakanin 1816 zuwa 1846. A zamaninsa ne Fulani makiyaya suka yi hijira zuwa Masarautar daga sassa daban-daban na yankin Arewa.
A bayansa akwai Malam AbdurRahman wanda ke kan karagar mulki tsakanin 1846 zuwa 1851, shi ma Mallam Abdulkadir ya gaje shi daga 1851 zuwa 1868. Lokacin da Abdulkadir ya rasu a 1868, Muhammad Hajiji ya gaje shi. wanda ya hau karagar mulki tsakanin 1868 zuwa 1896. Sauran sarakunan da suka biyo bayansu sun hada da: Abdulkadir (1896-1905), Muhammadu (1947).Wani abu mai ban mamaki da ya faru a zamanin mulkin Alhaji Muhammadu shi ne, a lokacin ne aka fara samun mota ta farko a garin Azare wanda a lokacin ya kasance hedikwatar masarautar Katagum bayan da Sarkin Katagum na tara Malam AbdulKadir ya cire shi daga Katagum a shekarar 1910 domin samun saukin gudanar da mulki.
A tsakanin 1947 zuwa 1980 Masarautar Katagum ta kasance karkashin Umar Faruk inda Mallam Abubakar ya gaje shi.
An nada Alhaji Muhammadu Kabir Umar ne a shekarar 1980. Masarautar tana da wuraren tarihi, wadanda suke jan hankalin masu yawon bude ido kamar tsaunin Shira da zane-zane da mutanen farko a yankin suka yi; kabarin Malam Lawan mahaifin Malam Zaki wanda ya kafa Katagum wanda yake a garin Yayu a gundumar Chinade; katangar tsaro a kauyen Katagum da kuma kabarin Malam Zaki wanda ke wajen katangar tsaro ta Katagum.
Addini
Manyan addinai guda biyu a Azare su ne Musulunci (kimanin kashi 90) da Kiristanci (kimanin kashi 10)
Al’adu
Al’adun mutane ya fi tasiri ne da mutunta Musulunci, al’adun aure na mutane yana bisa tsarin Musulunci. Misali, neman aure da yanayin sutura.
Noma
Wuri ne da ke da kasa mai albarka domin ayyukan noma masu kyau da ake samu a yankin sun hada da gero, gyada, masara, wake,Albasa, alkama, Auduga, kayan lambu, Dogon yaro (Bishiyar Maina) da kiwo.
Azare Ita ce mafi girma a cikin garuruwan da suke kusa da yankunan da suka hada da Jama’are, Misau, Bulkachuwa, Disina, Faggo, Zadawa Madachi,da Madara.
Azare gari ne da yake da cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, da kuma Kwalejin gwamnatin tarayya ta Azare, da kuma Kwalejin Ilimi ta Azare wadda mallakar gwamantain Jihar Bauchi ce.
Mutanen Azare yawacinsu Musulmai ne,wanda asalinsu Hausawa ne, kuma zuriyar kabilar Hausa ne. Babban aiki ko tattalin arzikin Tarihin
An samo wannan Tarihin ne daga encyclopedia ta Hausa