• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masarautar Saudiyya Ta Kere Elon Musk Da Bill Gates Arziki

Arzikin Masarautar Saudiyya Ya Zarta Na Masarautar Birtaniya Sau 16

by Sadiq
2 years ago
Saudi Crown Prince Mohammed bin Salman receives The President of the United Arab Emirates, Sheikh Mohammed Bin Zayed Al-Nahyan, in Jeddah, Saudi Arabia, July 16, 2022. Saudi Press Agency/Handout via REUTERS ATTENTION EDITORS - THIS PICTURE WAS PROVIDED BY A THIRD PARTY

Gidan Masarautar Saudiyya ya kere mamallakin X (twitter) da shugaban kamfanin Microsoft arziki a duniya, inda darajarsu ta kai dalar Amurka tiriliyan 1.4 (£1.1trillion).

MujallarForbes ta kiyasta arzikin Elon Musk, mamallakin X zuwa dala biliyan 251.3 (£ 191bn), yayin da Bill Gates, mai kamfanin Microsoft arzikinsa ya kai dala biliyan 119.6 (£93bn).

  • Wata Mata Ta Sace Jariri Sabuwar Haihuwa A Asibiti A Nasarawa
  • Harin Boko Haram Ya Yi Ajalin Mutane 7 A Yobe

Gidan sarautar Saudiyya ya hada da zuriyar Muhammad bin Saud, wanda ya kafa Masarautar Diriya a karni na 18.

Iyalan masarautar sun kunshi kusan dangi 15,000 – ko da yake dukiyar masarautar mutum 2000 ne ke juya ta.

Bangaren da ke mulki a masarautar ya fito ne daga zuriyar Abdulaziz bin Abdul Rahman, wanda ya zamantar da Saudiyya.

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Shugaban zuri’ar masarautar a yanzu shi ne Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, wanda hau karagar mulki tun a shekarar 2015.

Fitaccen dansa wanda kuma shi ne magajinsa; Mohammed bin Salman, wanda aka fi sani da MBS, Yarima mai jiran gado, wanda kuma shi Firaministan Saudiyya na yanzu wanda da yawa a kasar ke kallon sa a matsayin mai juya akalar mulkin Saudiyya.

MBS da Sarki Salman suna sa ido kan abin da ya shafi tafiyar da masarautar da abin da ya shafi tauye ‘yancin jama’a da ‘yancin siyasa.

Asalin arzikinsu ya samo asali ne daga man fetur da aka samo a kasar shekaru 70 da suka gabata, wato tun a zamanin Sarki Abdulaziz bn Saud.

Masarautar Saudiyya na boye bayanan arzikinsu da yadda suke tafiyar da harkokin kudadensu, amma yadda suke kashe kudade da tafiyar da rayuwarsu ya sanya a lokuta da dama hankalin jama’a ke zuwa kan su.

A halin yanzu, harkokin kudin gidan sarautar Birtaniya na ka terere daga kafofin watsa labarai da jama’a.

Kamfanin Brand Finance ya yi wa dukiyar masarautar da Sarki Charles III ke jagoranta kimar daraja dala biliyan 88 (£69bn).

Hakan na nufin arzikin masarautar Saudiyya ya ninka na dangin Sarki Charles na III sau 16.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin
Manyan Labarai

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Next Post
PDP A Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Sadiq Wali Da Abacha

Kotu Ta Raba Auren Shekaru 7 Saboda Rashin Soyayya

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.