Wata kotu da ke yankin Kubwa, Abuja ta raba auren shekara bakwai tsakanin Ramatu Ahmed da mijinta, Yahaya Salihu saboda rashin soyayya.
Alkalin kotun, Mohammad Wakili ya raba auren bisa ga dokokin Musulunci, bayan Ramatu ta bukaci hakan.
- Masarautar Saudiyya Ta Kere Elon Musk Da Bill Gates Arziki
- Dan Majalisa Ya Koka Kan Yawan Garkuwa Da Mutane A Kogi
Wakili ya kuma umarce da ta kiyaye dokokin “Iddah” na watanni uku bayan yanke hukunci kafin ta sake yin wani auren.
Tun da farko, matar mai ‘ya’ya biyu, ta shaida wa kotu cewa ta auri Salihu a shekarar 2017 kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada.
Ta ce ta shafe kusan shekaru shida tana fama da rashin soyayya wanda hakan ya sa ta bukaci a raba auren.
“Duk da shiga tsakani da iyaye suka yi, lamarin bai sauya ba, ba zan taba son Salihu ba ina son kotu ta raba auren,” in ji ta.
Ta kara da cewa a lokacin da mahaifinta ya rasu, Salihu ya je ya yi wa danginta ta’aziyya amma ya ki gaisawa da mahaifiyarta.
A martanin da ya mayar, Salihu ya ce ba ya son ci gaba da zama da matar tasa kuma ya amince da kotun ta raba auren.
Ya ce ya zauna da ita darajar mahaifinta da rasu wanda ya kasance tamkar mahaifina wajensa.