Masarautar Zazzau ta soke bikin hawan daba a bikin Babbar Salla mai zuwa.
Mallam Yusuf Abubakar Hayat, sakataren masarautar ne ya sanar da wannan mataki a cikin wata sanarwa da ya fitar.
- Masanin Afirka Ta Kudu: Huldar Kasarsa Da Sin Na Haifar Da Moriyar Juna
- An Daure Wata Mata Kan Yi Wa Yaro Dan Shekara 8 Fyade
Ya ce matakin ya zo ne bayan tafiyar da Mai martaba Sarkin Zazzau Mallam Ahmed Nuhu Bamalli ya yi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Sanarwar ta kara da cewa, Sarkin wanda tuni ya taya al’ummar masarautar Zazzau murnar barka da sallah, ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Nijeriya da su gudanar da addu’o’i don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Ana shafe tsawon kwana uku ana hawan dawaki a Masarautar Zazzau duk shekara, a wani bangaren na bikin babbar salla.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp