Masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da wasu wasu mutum biyu a wani rukunin gidajen sojojin Nijeriya da ke birnin tarayya Abuja, sun bukaci a biya su kudin fansa miliyan N30 don su sako wadanda suka yi garkuwa da su.
LEADERSHIP ta rawaito cewa abun ya faru a daren ranar Alhamis da misalin karfe 10 na dare lokacin da masu garkuwar suka kai hari gidan Cyril Adikwu da ke rukunin gidajen sojoji a Kurudu, Abuja.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Jama’a Da Dama A Rukunin Wasu Gidaje A Abuja
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Abuja, Sun Yi Garkuwa Da Mutane 9
Adikwu, wanda ya yi nasarar guduwa a lokacin kai farmakin, ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun yi magana da shi, inda suka bukaci a biya su makudan kudin fansa cikin kayyadadden lokaci, kamar yadda Businessday ta rawaito a ranar Asabar.
“Al’amarin ya faru a daren ranar Alhamis da misalin karfe 10:00 na dare, wata mota dauke da wadanda aka yi garkuwa da su ta shiga harabar gidana, sai kwatsam masu garkuwa da mutane suka biharabayo motar zuwa cikin harabar,” in ji Adikwu.
“Kusan su takwas ne, kuma sun bi ta hanyar daji da ke kan tudu zuwa wancan wurin, an kira ni ne domin in bayar da kudin fansa, ba na son na ambaci adadinsu, domin tuni bayanan karya ya cika ko’ina a kafafen yada labarai. duk abin da ya faru, amma ina tabbatar muku sun bukaci fiye da miliyan 30.”
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, lamarin yin garkuwa da mutane a Abuja ba wani abu ba ne sabo. Ko a makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane akalla 10 a unguwar Dutse-Alhaji da ke babban birnin tarayya Abuja, bayan da aka ce wasu ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji sun mamaye yankin.
Masu garkuwa da mutane sanye da kaya irin na makiyaya, an ce sun mamaye gidan ne da yamma da misalin karfe 7:30 na dare.
Wannan lamari dai na zuwa kwanaki kadan bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe wata budurwa mai suna Nabeeha Al-Kadriyar da suka yi garkuwa da ita da wasu mata guda biyar a birnin na Abuja.