BBC ta ce, Masu garkuwa da mutane sun kashe wasu ‘yan uwan juna su uku tare da wani mai babur bayan da suka karɓi fansar naira miliyan 60 daga mahaifin yaran a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kusa da dajin Garin Dogo a yankin ƙaramar hukumar Lau ranar Lahadi.
- Jami’an Tsaro Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Da Masu Garkuwa Da Mutane 12 A Bauchi
- Yadda Mai Juna Biyu Ta Rasa Ranta Wurin Ceton Mijinta Daga Hannun Masu Garkuwa
Rahotonni sun ruwaito cewa masu garkuwar sun kama mutanen uku – waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya – inda kuma suka buƙaci naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.
Mahaifin yaran uku wanda mai sana’ar safarar shanu ne ya daidaita da masu garkuwar – waɗanda suka amince zai biya su naira miliyan 60 domin sakin ‘ya’yan nasa uku.
Sai kuma ya ɗauki Ɗan Achaba tare da bashi kuɗin domin kai wa masu garkuwar a cikin dajin da ke kusa da ƙauyen nasu, dan sakin ‘ya’yan nasa .
To sai dai bayan kai kuɗin fansar da mai babur ɗin ya yi sai suka kashe shi tare da sauran yaran uku, bayan sun karɓi kudin fansar.