Wasu masu kwacen waya sun hallaka wata mata ‘yar shekara 58 a duniya, Aishatu Abdullahi, a gidanta da ke Jeka Da Fari ta jihar Gombe a daren ranar Juma’a.Â
An ruwaito cewa ‘yan daban sun mamaye gidan marigayiyar da misalin karfe 9:45 na dare domin yi mata fashi da makami.
- Rusau: Kotu Ta Gargadi Gwamnatin Kano Kan Rashin Bin Umarninta
- Da Kyar Nake Samun Yin Sallah Sakamakon Yawan Mutane Masu Korafi – El-Mustapha
A kokarin da suke yi na mata fashin wayar ne suka daba mata wuka da ya yi sanadiyyar ajalinta.
Lamarin da ya tada hankalin al’ummar unguwar.
Idan za a tuna dai a ‘yan watannin baya kadan wasu ‘yan daba sun shiga gidan fitaccen malamin addinin musulumci da ke jihar, Sheikh Albani Kuri, da manufar masa fashin wayoyi daga baya ma suka kashe shi sakamakon kin ba su wayoyin nasa.
Rundunar ‘yansandan jihar Gombe ta mika ta’aziyyarta da jimami dangane da kisan matar, inda ta sha alwashin binciko makasan a duk inda suke domin wanzar da adalci a tsakani.
A wata sanarwa dauke da sanya hannun kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Mahid Muazu Abubakar, da ya fitar a ranar Asabar, ta ce za su kamo makasan babu makawa.
Ya ce, “Kwamishinan ‘yansanda mai kula da sashen ayyuka na jihar Gombe CP Hayatu Usman a madadin kwamishinan ‘yansandan jihar Gombe ya umarci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ya tsaurara bincike kan kisan da aka yi wa Aishatu Abdullahi a ranar Juma’a.
“Bayan samun labarin faruwar lamarin, jami’an ‘yansanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru inda aka samu gawar Aisha kwance cikin jini, nan take aka garzaya da ita asibitin kwararru, a nan ne aka tabbatar da mutuwarta.”
Rundunar ta roki jama’a da su taimaka mata da bayanan yadda za a cafko makasan da sauran ayyukan ta’addanci a jihar.
Shi ma, gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi tir da Allah wadai da kisan matar.
A wata sanarwa dauke da sanya hannun babban hadimin gwamnan a bangaren yada labarai, Isma’ila Uba Misilli, gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta kamo makasan.
Ya mika ta’aziyyarsa da addu’ar Allah jikan mamaciyar.
Gwamnan ya tabbatar da cewa ba za su taba bari jininta ya tafi a banza ba.