A ranar 24 da yamma, bisa agogon wurin, wasu mambobin kungiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin 3 sun shiga cibiyar bincike ta Huanghe ta kasar Sin dake tsibiran Svalbard na kasar Norway, inda za su gudanar da dimbin ayyukan bincike cikin fiye da watanni 7 dake tafe.
A cewar He Fang, shugaban cibiyar bincike ta Huanghe, ana sa ran ganin Sinawa masu nazarin kimiyya da fasaha 41 zama a cibiyar a bana, inda za su aiwatar da binciken da ya shafi manyan ayyukan nazari guda 9, da suka jibanci fannonin halittu na kasa da na teku, da ilimin kimiyyar lissafi (Physics) mai alaka da sararin samaniya, da sa ido kan yanayin kankara, da dai makamantansu. Ban da haka kungiyar nazari ta Sin za ta yi hadin gwiwa tare da bangaren Norway, don gudanar da nazari na hadin gwiwa kan wasu abubuwan da ke gurbata muhallin yankin Arctic. (Bello Wang)