Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC sun yi kira ga shugabannin jam’iyyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da su dauki gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum a matsayin wanda zai yi wa Bola Ahmed Tinubu takarar mataimaki a zaben 2023.
Gamayyar masu ruwa da tsakin su 840, sun yi imanin cewa idan aka dauki Zulum za ta taimaka wa jam’iyyar wajen samun nasara a babban zabe mai zuwa na 2023, tare da taimakawa a kokarin ceto kasar nan daga durkushewa.
- Farashin Gas Din Girki Ya Kara Yin Tashin Gwauron Zabi — NBS
- Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi, Sule Da Sanata Jika Sun Fice Daga Jam’iyyar APC
Shugaban kungiyar na kasa, Abdullahi Aliyu Katsina, a lokacin da yake jawabi ga shugabannin jihohi bakwai na Arewa maso Yamma a Jihar Katsina a ranar Lahadi, ya bayyana cewa Zulum ne kadai wanda ya sace zukatan ‘yan Nijeriya ta hanyar jagoranci nagari a cikin shekaru uku da suka wuce.
A cewarsa sadaukarwar da gwamna Zulum ya yi a Jihar Borno, ta isa jam’iyyar APC ta ba shi damar hidimtawa Nijeriya.
Har wa yau, ya ce ya yi imanin Zulum ne wanda ya fi dacewa da gurbin takarar mataimakin shugaban kasa.
“Bukatar mu a bude take kuma bai wuce daukar gwamna Zulum na Jihar Borno a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba.
“Mun fahimci cewa gwamna Zulum ne kadai zai iya kawo kuri’u daga jihohin Arewa 19.
“Don gudun kada a fadi zabe, a yau mutum daya tilo a Nijeriya wanda zai iya kawo wa jam’iyyar nan nasarar da ake bukata shi ne gwamna Zulum. Duk wanda a yau aka zaba a matsayin mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, in ba Zulum ba, ba zai iya kai mu ga gaci ba.
“Rashin zabar Zulum, zai iya kai mu ga faduwa zabe.”