Ɗaruruwan masu sana’ar kamun Kifi a Jihar Taraba, sun koka kan raguwar samun kudaden shiga, sakamakon rashin samun wadatattun Kifayen da suke kamawa.
Wani bincike ya nuna cewa, a wasu shekarun baya; a kullum masu sana’ar na samun kudaden shiga daga kimanin Naira 10,000 zuwa Naira 20,000, amma yanzu sai da kyar suke iya samun Naira 10,000 a kullum.
- Gwamnatin Kebbl Ta Dage Bikin Kamun Kifi Karo Na 61 Na Argungu Har zuwa Shekarar 2026
- Shugaban Ghana Ya Kaddamar Da Tashar Ruwa Ta Kamun Kifi Wadda Kamfanin Sin Ya Tallafa Wajen Gina Ta
Wasu rahotanni sun nuna cewa, sama da shekarun da suka gabata, kamun Kifi na kara raguwa, wanda hakan ya tilasta wasu masu sana’ar komawa yin noma da kuma kama wasu sana’oin daban, don ci gaba da kula da rayuwarsu.
Kazalika, masu sana’ar da suka dogara kan sana’ar a kanannan hukumomi 12 na jihar, kudaden shigar da suke samu na kara raguwa.
Bincike ya nuna cewa, ana samun raguwar kamun Kifin ne, bisa abubawa da dama da suka hada da; amfani da wasu sinadaran kamun Kifin ba bisa ka’ida ba, sauyin yanayi da sauransu, wanda hakan ya haifar da raguwar yawan Kifi a Koguna.
daya daga cikin masu sana’ar a yankin Yashin Tuwo a karamar Hukumar Karim-Lamido a jihar, Mallam Dauda Adamu, ya tabbatar da wannan kalubalen da masu sana’ar ke fuskanta a jihar, inda ya sanar da cewa, lamarin ya tilasta wasu masu sana’ar rungumar aikin noma da kama wasu sana’oin daban, domin samun kudaden shiga.
“A baya masu sana’ar a kullum suna samun kudaden shiga masu yawan gaske, sai dai; saboda raguwar Kifin a Koguna, kudaden shigar da suke samu sun ragu”, in ji Dauda.
Wani jami’i a Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar, wanda bai bukaci a ambaci sunansa ba, ya tabbatar da wannan raguwa ta Kifin a Kogunan jihar.
Kazalika, Mallam Dauda ya alakanta wannan kalubalen kan irin yanayin kamun Kifin da masu sana’ar ke yi, samun sauyin yanayi da kuma yin amfani da wasu sinadaran kamun Kifin da masu sana’ar ke yi a jihar, wadanda ya ce, su ne manyan ummul haba’isin matsalar da ta shafi fannin.
Ya bayyana cewa, za a iya magance wannan matsalar, a kwanakin baya; Ma’ikatar Aikin Gona ta jihar, ta kaddamar da gangamin ilimantar da kan masu sana’ar kamun Kifin a jihar, musamman kan kamun Kifin ba bisa ka’ida ba.
Kazalika, Mallam Dauda ya ce; ma’aikatar ta kuma raba wa masu sana’ar kamun Kifin ingantattun Rigar kamun Kifin da kuma sauran kayan aikin kamunsa, domin daina yin kamun Kifin ba bisa ka’ida ba.