Zahra’u Adam Matashiya ce mai hazaka da jajircewa kan neman ilimi, inda ta shawarci mata da su dage da karatu domin a cewarta idan mata suka yi karatu za su taimakawa kansu da ‘ya’yansu, baya ga haka ta bayyana wa wakiliyarmu BILKISU TIJJANI KASSIM, irin nasarori da kalubalen da ta fuskanta, kamar dai yadda za ku karanta kamar haka:
Da farko za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Sunana Zara’u Adamu Sulaiman, an haife ni a garin Hadejia, na yi primary da sikandire a Usman bin Affan, kuma na yi sikandire a GGDSS Hadejia yanzu ina NCE a College Of Education Legel Studies.
Zara’u kina da aure ce?
A a bani da aure
Malama Zara’u kina da wata sana’a ne ko kuma karatun aka sa gaba?
A’a gaskiya kasancewar ni daliba ce, gaskiya ni ba ni da wata sana’a, sai dai karatu, shi na sa a gaba, tukunnan sana’a, sai mun kammala karatu in sha Allahu.
Me kike karanta?
Ina karantar fannin Tattalin Arziki da Turanci
Me yaja hankalinki da har kike sha’awar wannan karatun wadannan fannoni?
Saboda ina da sha’awar sanin harkokin kasa ciki da waje, sannan in san yadda ake tattalin arzikin kasa da na gida musamman ma ina ganin ni mace ce da zan rike gida.
Idan na iya tattala kayan gida, na iya adana su ba’a almabozarancin su, to ina ganin wannan ma yana da kyau.
Sannan idan na karanci tattali zan san abubuwan da suka shafi kasa, abubuwan da ya kama a yi a kasa da wanda bai kamata ba. Za ka gane yadda ake lafiyar da kasar ya yi daidai ko bai yi ba.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin karatunki?
Zngon karatuna na biyu, a matakin karatuna na uku na fiuskanci kalubale da dama, wanda sai dai na yi addau’a da fatan kada na sake samun irin wannan abin, Allah ya kiyaye mana gaba.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika samu?
To Alhamdulillah ka ga komai naka yana tafiya yadda ya kamata, karatun na babu wata matsala, to wannan ba karamar nasara bace a wajena, gashi yanzu har mun kawo shekara ta karshe, muna zango na karshe kwanaki kadai ya rage mu kammala ai sai dai na ce Alhamdulillah.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da karatunki?
Abin da yafi faranta min rai game da karatuna, shi ne na shiga jarabawa na ga na gane kowace tambaya, a gasukiya wannan ba karamin jin dadi nake ba, yana farantamin rai sosai.
Dame kike so mutane su rika tunawa dake?
Ina so mutane su rinka tunawa da ni akan hakuri na da son zaman Lafiya.
Wanne irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
A ce Allah ya yi min albarka ya kuma jikan mahaifana a gaskiya ina jin dadin wannan addu’ar sosai kuma tana birge ni.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Ina samun goyon baya daga wajen iyaye na sosai da sosai, saboda su ke karfafa min gwiwa wajen na jajirce akan karatu na, kuma su suka saka ni a makaranta tun ina karama har na kawo yanzu, to babu abin da zan ce da su sai godiya, ina gode wa Allah Alhamdulillah, sannan ina gode wa iyayena sosai.
Kawaye fa?
Kawata daya ce mai suna zaliha, muna tare da ita muna karatu.
Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Cikin kayan sawa ina son dogowar riga ta yadi, kayan kwalliya kuma gaskiya ni ba ma’abociyar kwalliya bace.
A karshe wanne irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Shawarata a gareku ‘yan uwana mata ku dage da karatu domin tallafawa rayuwarku da ta ‘ya’yanku