Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing, ya bukaci a aiwatar da dukkanin matakan ceto, sakamakon aukuwar ambaliyar ruwa da ta haddasa bacewar mutane sama da 30 a lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar.
Zhang Guoqing, ya yi kiran ne a jiya Lahadi, yayin da ya ziyarci kauyen Xinhua na gundumar Hanyuan dake karkashin birnin Ya’an wanda ibtila’in ya aukawa, inda ya zagaya asibitin dake wurin da kuma matsugunnin wucin gadi da aka tanada domin wadanda ambaliyar ta raba da muhallansu.
- Taron JKS: Kudurin Kara Zurfafa Gyare-gyare Zai Sa Kaimin Aikin Zamanintar Da Sin
- Kamfe: An Tara Wa Kamala Haris Kusan Dala Miliyan 50 Cikin Sa’o’i 2 A Amurka
Har ila yau, Zhang ya jagoranci wani taro da yammacin jiyan, inda ya bayyana cewa aikin dake kan gaba, shi ne lalube da ceto wadanda suka bace, kuma za a kara adadin kwararru don gaggauta nasarar hakan.
Daga nan sai ya bayyana bukatar samar da kudaden sassauta radadin ibtila’in, da kayayyakin bukata a kan lokaci, da karfafa hidimomin kula da lafiya a wuraren da aka tsugunar da mutane, da tabbatar da cewa mazauna wurin na samun isassun kayayyakin bukata na rayuwa, da dawo da gudanar da ayyuka da tsarin rayuwa ba tare da bata lokaci ba.(Saminu Alhassan)