• English
  • Business News
Tuesday, July 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taron JKS: Kudurin Kara Zurfafa Gyare-gyare Zai Sa Kaimin Aikin Zamanintar Da Sin

by Abdulrazaq Yahuza
12 months ago
in Ra'ayi Riga
0
Taron JKS: Kudurin Kara Zurfafa Gyare-gyare Zai Sa Kaimin Aikin Zamanintar Da Sin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Na fara sanin manufar gyare-gyare da bude kofa ta kasar Sin a lokacin da aka yi bikin cikar manufar shekaru 40 da kafuwa a shekarar 2018. Rahotannin da na gani a game da ci gaban da manufar ta kawowa kasar da sauran kasashen da aka yi kawancen ci gaba tare da su, a karkashin tsare-tsare daban-daban kamar na Ziri Daya da Hanya Daya (BRI), Dandalin Kawance na FOCAC, sun nuna kyakkyawar alkiblar da Sin ta dosa.

Manufar wadda a bana ta cika shekaru 46 da kafuwa ta kara samun tagomashi yayin da zaman taro na uku na Kwamitin Kolin Jam’iyyar Kwaminisanci ta Kasar Sin (JKS) karo na 20 ya amince da kudurin kara zurfafa gyare-gyare don habaka zamanintar da kasar, a birnin Beijing, kwanan nan.
Babban burin da ake neman cimmawa a kokarin da ake na kara zurfafa gyare-gyare, shi ne ci gaba da ingantawa da raya tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, da kuma zamanintar da tsarin gudanarwa na Sin da karfin iya shugabanci.

Da yake masu magana kan ce “aiki ga mai kare ka”, ana sa ran nan da 2035, Sin za ta kammala gina tattalin arzikin kasuwanci irin na gurguzu mai matukar inganci a dukkan fannoni. Tabbas hakar kasar za ta cimma ruwa bisa yadda ta sha damarar ganin an sauke duk wani nauyi da ya rataya ga samun nasarar kudurin a yayin da Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin za ta yi bikin cikarta shekara 80 da kafuwa a 2029.

Ba kanta kadai take kallo ba, a duk harkokin ci gaba da wayewa irin na zamani mai inganci da babu coge a ciki, kasar Sin tana duba al’ummar duniya a matsayin wadanda za a gudu tare, a tsira tare. Shi ya sa, sanarwar bayan taron JKS ta jaddada cewa, tsarin zamanintar Sin shi ne tsarin bunkasa zaman lafiya a zamanance, domin “a huldar dake tsakanin kasashen waje da kasar Sin, kasar ta tsaya tsayin daka wajen aiwatar da manufar zaman lafiya mai cin gashin kanta, kana ta himmatu wajen inganta al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya,” in ji sanarwar.

A aikace, an ga irin kokarin da Sin take yi a manufofinta na bude kofa da zaman lafiyar duniya ta hanyar kai ci gaban tattalin arziki maimakon tayar da husumar yake-yake a kasashe daban-daban da kuma jawo su a jiki su shigo cikinta domin cin moriyar juna. Wannan ya tsayawa kasashen yamma a kahon zuci, shi ya sa duk abin da kasar ta kawo sai an shafa masa kashin kaji ta hanyar kushe manufar bude kofar da kuma yayata farfaganda a kafafen yada labarunsu daban-daban cewa, manufar tana samun koma-baya da rashin karbuwa a duniya.

Labarai Masu Nasaba

Kayayyakin Sin Na Kara Samun Karbuwa A Kasuwar Duniya

Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa

To sai dai, a gaya musu “kifi na ganin ka mai jar koma”, domin kasar Sin ta ci gaba da rike kambunta na zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya da zama kasar da ta fi yawan cinikin hajjoji a cikin shekaru bakwai a jere, da ci gaban da ta samu na hada-hadar tattalin arzikin cikin gida a rabin farko na bana da ya kai fiye da Yuan tiriliyan 61, wanda ya karu da kashi 5 idan aka dora a sikeli da na bara war haka.

Bisa jajircewar Sin a karkashin shirinta na bude kofa na zamani, ta ci gaba da fadada huldar kasuwanci da kasashen duniya. Kasuwancin da take yi a karkashin hadin gwiwar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) ya karu da kashi 7.2, a rabin shekarar 2024.

Bayan haka, Sin ta kara yawan kasashen da take sahale musu shiga cikinta ba tare da biza ba. A tsakanin wata shida na 2024 kacal, a kalla ’yan kasashen waje miliyan 14 suka shigo cikinta, kusan adadin da ya ninka wadanda suke shiga duk shekara.

Wadannan misalai sun isa su nuna karbuwar da manufar bude kofar Sin ke samu tare da fadada damammakin zuba jari ga ’yan kasashen waje a cikinta.

A bisa tsare-tsaren kara zurfafa gyare-gyare da taron JKS ya aminta da su, tabbas ba Sin kadai za ta ci gajiyar wadannan gyare-gyare ba har da sauran kasashen duniya bisa manufarta ta bude kofa, ba kamar masu tsuke kasuwanninsu na shigo da kaya da fadada na fitarwa kamar yadda su Amurka ke yi ba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: bude kofaCi Gabagyare-gyareJKSSinTaro
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Kama Wanda Ya Kitsa Kashe Janar Udokwere A Kano

Next Post

Kamfe: An Tara Wa Kamala Haris Kusan Dala Miliyan 50 Cikin Sa’o’i 2 A Amurka

Related

Kayayyakin Sin Na Kara Samun Karbuwa A Kasuwar Duniya
Ra'ayi Riga

Kayayyakin Sin Na Kara Samun Karbuwa A Kasuwar Duniya

4 days ago
Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa
Ra'ayi Riga

Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa

5 days ago
Kayan Aro Baya Rufe Katara
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa JKS Mai Tsawon Tarihin Sama Da Shekaru 100 Ta Dore A Kan Mulki

6 days ago
Wannan Imanin Ne Ya Kai Likitocin Sin Nahiyar Afirka…
Ra'ayi Riga

Wannan Imanin Ne Ya Kai Likitocin Sin Nahiyar Afirka…

2 weeks ago
Nuna Karfin Tuwo Ba Zai Kawo Zaman Lafiya Ga Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
Ra'ayi Riga

Nuna Karfin Tuwo Ba Zai Kawo Zaman Lafiya Ga Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba

2 weeks ago
Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
Ra'ayi Riga

Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya

3 weeks ago
Next Post
Kamfe: An Tara Wa Kamala Haris Kusan Dala Miliyan 50 Cikin Sa’o’i 2 A Amurka

Kamfe: An Tara Wa Kamala Haris Kusan Dala Miliyan 50 Cikin Sa'o'i 2 A Amurka

LABARAI MASU NASABA

Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Nijeriya Ba Ta Da Sha’awar Yin Gwajin Makamin Nukiliya — Shettima

July 8, 2025
Da Ɗumi-Ɗumi: Osimhen Ya Amince Da Komawa Galatasaray Na Dindindin

Da Ɗumi-Ɗumi: Osimhen Ya Amince Da Komawa Galatasaray Na Dindindin

July 7, 2025
Sin Za Ta Ci Gaba Da Karfafa Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Kan Tinkarar Sauyin Yanayi

Sin Za Ta Ci Gaba Da Karfafa Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Kan Tinkarar Sauyin Yanayi

July 7, 2025
Ƙungiyar Al’ummar Igbo Ta Ohanaeze Ndigbo Ta Ce Tinubu Ya Fi Ƙarfin ‘Yan Jam’iyyar Haɗaka Ta ADC

Ƙungiyar Al’ummar Igbo Ta Ohanaeze Ndigbo Ta Ce Tinubu Ya Fi Ƙarfin ‘Yan Jam’iyyar Haɗaka Ta ADC

July 7, 2025
Sin Za Ta Gina Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Ingantaccen Lantarki

Sin Za Ta Gina Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Ingantaccen Lantarki

July 7, 2025
NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19

NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19

July 7, 2025
Sin Ta Kafa Kungiyar Masana Masu Binciken Sararin Samaniya Mai Zurfi Ta Farko

Sin Ta Kafa Kungiyar Masana Masu Binciken Sararin Samaniya Mai Zurfi Ta Farko

July 7, 2025
Xi Ya Ajiye Furanni Ga Wadanda Suka Mutu Yayin Yakin Bijirewa Harin Japan

Xi Ya Ajiye Furanni Ga Wadanda Suka Mutu Yayin Yakin Bijirewa Harin Japan

July 7, 2025
Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Aikin Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%

Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Aikin Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%

July 7, 2025
Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista

Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista

July 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.