Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing ya yi kira da a yi kokarin gaggauta bunkasa masanaantun samar da fasahar intanet ta 5G.
Zhang ya bayyana haka ne a yayin bikin bude taron masanaantun yanar gizo na 5G+ na kasar Sin da aka gudanar a birnin Wuhan na lardin Hubei dake yankin tsakiyar kasar.
- Sin Ta Taimaka Wajen Gudanar Da Shirin Horas Da Daliban Jami’ar IPRC Ta Rwanda
- Ana Fatan Sakamakon Ganawar Xi Da Biden Zai Taka Rawa Wajen Kyautata Dangantakar Sin Da Amurka
Ya ce, manufar wannan kokari ita ce, inganta sabbin masanaantu da gina tsarin masanaantun kasar na zamani.
Mataimakin firaministan ya ce, yayin da ake ci gaba da zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki na zamani da sashen samar da kayayyaki da na hidima, ya kamata kasar ta hanzarta yiwa masana’antun garambawul, da inganta su da fasahohin zamani, da intanet da fasahohin kwaikwayon tunanin dan-Adam.
Ya ce, ya kamata a zage damtse don inganta kayayyakin intanet, da hanzarta amfani da fasahohin intanet da ma karfafa tsaron fasahar. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)