Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, kuma jagoran harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin Amurka, ya tattauna ta kafar bidiyo tare da sakataren baitulmalin Amurka Scott Bessent da kuma wakilin kasuwanci na Amurka Jamieson Greer a jiya Jumma’a.
Bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayoyi mai zurfi kan aiwatar da muhimmiyar yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a lokacin ganawarsu a Busan da kuma tattaunawar wayar tarho da suka yi ranar 24 ga watan Nuwamba, kana da inganta hadin gwiwa mai amfanarwa tare da magance matsalolin da suka shafi tattalin arziki da cinikayya yadda ya kamata.
Bangarorin biyu sun yi maganganu masu alfanu game da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a Kuala Lumpur. Sun bayyana cewa, a karkashin muhimmin jagorancin shugabannin kasashen biyu, za su yi cikakken amfani da tsarin hanyoyin tuntuba kan tattalin arziki da cinikayya na Sin da Amurka, kana za su ci gaba da tsawaita jerin hadin gwiwa da kuma rage yawan matsalolin da ke kasa, da kuma karfafa ci gaban tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka mai dorewa ba tare da wata tangarda ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














