Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dass ta jihar Bauchi, Yunusa Umar, ya jagoranci mambobi fiye da 7,500 zuwa jam’iyyar PDP. Cikin waɗanda suka sauya sheka har da Shugaban Matasa na APC a yankin, Yusuf Inuwa Bora, da Sakatare mai kula da jin daɗin mambobi, Isah Zakaria.
An karɓi waɗannan sabbin ‘yan jam’iyyar ne a hukumance a ranar Lahadi, inda Shugaban PDP na ƙaramar hukumar Dass, Hon. Yusuf Sabo, da Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Mohammed Abubakar Jibo, suka tarɓe su. Umar ya bayyana cewa kyakkyawan shugabancin Gwamna Bala Mohammed ne ya sa suka bar APC.
- Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota
- Gwamnan Bauchi Ya Rantsar Da Mashawarta 11, Ya Horesu Da Aiki Tuƙuru
Ya jaddada cewa manufofi da shirye-shiryen gwamnan tun bayan hawansa mulki a 2019 sun amfanar da al’umma matuƙa. Ya ce suna da yaƙinin cewa PDP ce ke kula da walwalar jama’a, don haka ba su da dalilin ci gaba da zama a APC. Ya kuma tabbatar da cewa sabbin mambobin za su yi aiki tuƙuru don cigaban PDP a jihar.
Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Jibo, ya bayyana wannan sauya sheƙar a matsayin babbar nasara ga PDP, yana mai cewa gwamnatin Bala Mohammed za ta ci gaba da ɗorewa kan hanyoyin cigaban jihar Bauchi. Ya kuma tabbatar wa sabbin mambobin cewa za su samu cikakkiyar damar zama ‘yan PDP ba tare da nuna bambanci ba.