Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gana da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Paul Mashatile, a birnin Beijing a yau Alhamis.
Mista Han ya yi kira ga bangarorin biyu da su kara aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara nacewa ga zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da ci gaba da bunkasa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, da hidimta wa kokarin zamanantar da kasashen biyu.
A nasa bangaren, Mashatile ya ce, Afirka ta Kudu na matukar dora muhimmanci kan dangantakar da ke tsakaninta da kasar Sin, kuma tana ci gaba da yin tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya. Yayin da yake lura da cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu a fannonin ciniki, da zuba jari, da sauran fannoni sun samu ci gaba sosai, Mashatile ya ce, a shirye suke su kara aiwatar da matsayar da aka cimma ta bayar da gudummawa ga yaukaka zumuncin Afirka ta Kudu da Sin, har ma da na nahiyar Afirka da Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp