- Shugaba Buhari Ya Sa A Raba Tirelar Abinci 400
- Ba Cikin Dare Ko A Rami Muke Rabo Ba, Kowa Na Gani
- Zargin Da Gwamnan Benuwai Ya Yi Ba Gaskiya Ba Ne
- Allah Ya Wanke Mu Daga Zargin Boye Tallafin Korona
Ambaliyar Ruwan da ta auku a daminar da ta gabata ta 2022 ta haifar da barna mai dimbin yawa a Nijeriya inda aka yi kiyasin cewa ta shafi akalla mutum miliyan uku da dubu dari biyu da shatara da dari bakwai da tamanin, inda sama da miliyan daya kuma suka rasa muhallansu baya ga gonakai sama da hekta dubu biyar da al’amarin ya shafa da sauran asarori daba-daban.
Yanzu haka dai ma’aikatar kula da al’amuran jin kai ta kasa ta dukufa rabon kayan tallafi ga wadanda abin ya shafa. MINISTAR JIN KAI, HAJIYA SADIYA FAROUK ta yi wa wakilinmu na fadar shugaban kasa, JONATHAN INDA-ISAIAH bayani a kan tallafin da ake yi da matakan da aka dauka na magance karincin abinci a Nijeriya sakamakon ambaliyar da kuma hanyoyin da ma’aikatar ke bi wajen ganin ba a maimaita handama da babakere na kayan tallafin ba kamar yadda aka gani lokacin rabon tallafin Korona. Ga dai yadda hirar tasu ta kasance kamar yadda RABI’U ALI INDABAWA ya rubuta:
Ambaliyar ruwa kusan ta auku a kowace kusurwa ta kasar nan, ko za ki bayyana wa masu karatu ayyukan jin kai da kuke yi?
Kamar yadda ka sani wannan ambaliya ta faru tsakanin wannan watan da ya wuce, watan Satumba da karshe zuwa Oktoba, kuma garuruwa da dama a fadin kasar nan wannan ambaliya ta shafe su, mun zo mun ba da bayani kan abin da gwamnatin tarayya ta yi na magancewa da ganin an kawo sassauci ga wannan abu da ya faru, saboda ambaliya ta zo wa mutane da yawa, jama’a sun rasa gonakinsu wasu ma sun rasa rayukansu, wasu kuma sun rasa hanyar cin abincinsu.
Gwanatin Tarayya a karkashin ma’aikatata ta ba da tallafin agaji ga wadanda abin ya shafa, wannan shi ne abin da muka zo muka fada muku masu yada labarai don ku san abin da muke yi a gwamnatance.
Akwai tsoro da ake cewa wannan ambaliya za ta haifar da karancin abinci, ko me kuke yi a gwamnatance?
Abin da muke yi a yanzu shi ne, muna zuwa daukar alkaluma don mu ga iya yadda yawan abin yake, kuma a zauna a fidda manufofi daban-daban na ganin ba a kai ga wannan hali na karancin abinci ba, kamar yadda ka sani, akwai noman rani da za a yi wanda shi ne za mu ba da muhimmanci a kai kwarai da gaske a ga cewa an taimaka wa manoma an tallafa musu domin su yi noman rani ko ina a kasar nan.
Akwai bayanai da kuka yi wa mutane na cewa su lura da abin da ya faru kafin aukuwarsa?
An yi bayanai da dama babu iyaka ta kowane fanni, kafofin yada labarai daban-daban, mun isar da shi a gwamnatance, mun isar a al’umance, mun isar da shi a kungiyance, a ma’aikatata da ma’aikatar samar da albarkatun ruwa, da kuma ta masu sanin yanayi, su ma sun fitar da wannan kashedin, cewa wannan abu zai faru a wadannan jihohi kuma ga abin da zai biyo baya, to amma ga yadda lamarin yake, wasu sun ji wasu basu ji ba, abin bakin ciki har wasu mutane sun rasa rayukansu bisa wannan.
Amma fa kamar yadda ka sani ita ambaliya ba aba ce wadda za a iya hanawa ba, in dai za ta zo, to dole za ta zo. Abin da yake muhimmi shi ne a dauki matakan da ya kamata a dauka domin a samu sassauci ga faruwarta ya zama idan ta zo ba za ta tafi da rayuka ba kamar yadda muka gani, kuma wadanda ya kamata su yi abin da ya kamata, su yi.
Lokacin Korona mun ga yadda ma’aikatarki ta rika ba da tallafi, amma kuma sai aka samu wasu bata-gari suka rika almundahana da akai, a wannan lokaci wane mataki kuka dauka wajen ganin abin da kuka bayar ya isa hannun talakawa ba tare da ana cin dunduniyarku ba?
Gaskiya kam mun dauki matakai koacin Koronan nan duk da Allah ya wanke mu daga baya amma dai ba za mu so irinsa ya kara faruwa ba.
Matakin da muka dauka na farko shi ne, mun je mun fitar da kungiyoyi a kowace jiha da suka hada da kungiyoyin addini da kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin al’umma, da Red Cross, duka aka rubuta musu cewa za mu zo wannan jiha kuma ga kayan abincin da za mu kawo kuma ga kayan tallafin da za mu kawo, kuma za mu kawo wa mutum kaza, to wannan ya magance kuma ina ganin zai ci gaba da magance irin wannan abin da ya faru a baya a ga cewa duk abin da aka tura ya isa ga wadanda ake nufi a kan idon kowa kuma a kan idon mutanen da aka ce za a ba wa wannan taimako.
Kayan tallafin da aka raba ya kai Tan nawa?
To kamar yadda muka fada, shugaban kasa ya ba da umarnin cewa ma’aikatar gona ta ba mu abincin da yake rumbu kamar Tirela 400 kenan na kayan abinci wanda kuma mun raba shi kuma muna cikin rabawa. Sannan ban da wadansu kayan abincin da ma’aikatar NEMA ta saya, sannan kuma akwai kayan ma da ba na abinci ba kamar kayan shimfida da sauran kayan rayuwa na yau da kullum.
Gwamnan Benuwai yana ta korafin cewa gwmanti ba ta taimaka masa ba, ko za ki yi bayani a kan wannan?
To Jihara Beniwe dai kam ba karamin taimako muka ba wa jihar ba, duka ma’aikatun da ke karkashin ma’aikatata kafin ma ambliyar ruwan nan mun kai taimako Jihar Beniwai. Beniwai tana cikin jihohin da NEMA ta kai wa abin da ake cewa (Freefair), su aka fara kai wa a duk fadin kasar nan da suke amfani da shi wanda yanzu ake tunanin a kai wasu ma jihohin Kudu. To abin da muke yi ba cikin dare muke yi ko cikin rami ba kowa yana gani, kuma muna ajiye dukkanin bayanai, wannan ba Beniwai ba ne kadai ba duk inda abu ya faru muna kai taimako.
Ana siyasantar da wannan abin, wasu gwamnoni suna ganin kamar ba a yi komai ba, ku ma kuna kallon siyasar?
Aikinmu ba na siyasa ba ne, aikinmu na taimakon Dan’adam ne ga wanda Ibtila’i ya afka masa mu taimaka masa, ma’aikatarmu sunanta Ma’aikatar Ba Da Agajin Gaggawa da Jin Kai, abin da ban mamaki manya su fito suna cewa haka amma mun yi.