• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matan Kabilu Sun Fi Na Hausawa Juriyar Neman Na Kansu —Fatima Lawal

by Basira Nakura
3 years ago
Fatima Lawal

Cigaba daga makon jiya…
A wannan makon mun kawo muku cigaba da hirra da wakiliyarmu Basira Nakura ta yi da hazikar Malama data shahara wajen tarbiyantar tare da ba mata shawarar yadda za su yi zaman aurensu ba tare da wata matsala ba, wato Hajiya Fatima Lawan. Ga dai yadda hirara ta kasance.

To wane kira zaki yi ga mata ko ince wace shawara zaki baiwa mata ta bangaren gyara domin in muka yi duba ga matan kabilu sai kiga basa yi wa aure rikon da matan mu na Hausawa suke yi abin mamaki zaki samu sun fi namu matan ta kowane fanni, wani namijin ma idan ya auro kabila sai kiga har gorantawa mata ya ke yi idan ya auro kabila ta bangaren abinci ne tarairaya, kula da miji juriya da kowane fanni ma ko menene dalili?

To ai gaskiya Malama abin da yake kawo haka matan kabilu suna da juriya kuma suna neman na kansu, mafiya yawa matanmu na Hausawa cima zaune ne, mace ba za ta sayi ashana ta naira ashirin ta raba ta gida biyar taci naira biyar ba za ta yi wannan ba ko kuma ace mace tatattali kanta da abinci da mijinta ya kawo idan tasan cewar yau munacin gwangwani biyar a gidan yau an rage wani ba za fa ta yi tunanin cewar bari ta rage ba ace yara uku ne ga miji gani bari in miki wani misali ‘ya’ya biyu sun tafi unguwa kuma za ta dafa gwangwani biyar wai bata da kwakwalwar da za ta yi tunani bari in debe danyar nan in ajiye, a’a sai a jangabata a dafa azo kuma a barta a wulakance wanda idan da ta debe gwangwani biyu ta ajiye a matsayin mijinta mai karamin karfi gobe ma ace ta kuma yin haka to koda bako suka yi za su iya karawa da wannan sai kiga abu ya yi kyau to wata idan ta rage sai dai takai kasuwa to ina albarka a wannan, to shi kuma in har mace bata tsara kanta ba daman ance khairun nisa’i ala gaiz (mafificiyar mace mai yanga) ma’ana mai kiyaye kanta ta ita tsari ta iya magana ta iya girki ta iya kwalliya a aure ma inka aure ta sai kasan ka yi aure da mace saboda ta iya gyara kanta koda lokacin al’adarta ta yi al’adar ta ta gama tasa ruwa ta jangaba ta wanke sam ba haka ba ne za ta nemi abubuwa da ake nema na gyara kai ta gyara kanta ta yi matsi wannan matsin afuwan ku yi hakuri yana da nauyi wannan matsin da mace take yi shi yake jawo zuciyar da namiji matukar namiji bai ji al’aurarsa ta kame a jikin mace gamgam ba zuciyarsa ba za ta tattara a gurinta ba inda take sakaf haka shima zai ji sakaf a zuciyarsa amma inta matse ya ji wannan kamun to shi ne kamar mallakarsa ta kame kanta duk sanda ya zo zai ji saukinta da dokinta ya kamashi amma saboda Allah ya ga ya wuce kamar rariya a guje saboda Allah taya ba zai rainata ba fisabilillahi, ta bar kanta ta ragwargwaje yarinya karama ta zo tana tsami karasa me ma ya kawo wannan tsamin kai ya dade a kitse ana makamar ruwan wanka kuma ba wanke shi za a yi ba, ta ya ba zaki yi tsami ba an fito daga wanka an daure shi da danshinsa ba tare da ya sha iska ba ya hadu da fatar kai dole ne ya bada wani yanayi na dabam wani yanayi ma taci abinci ta kwanta ba ta yi ‘brush’ ba wata ma ko kuskure bakinta ba za ta yi ba domin a ka’idar yin ‘Brush’ ma in ta yi da daddare indan za ta kwanta da safe ba sai ta yi ba kuma shi yin ‘Brush’ ma ana so idan an yi abada kamar tazarar minti 30 kafin aci abinci bawai da an yi amaka abinci a baki ba saboda haka indai ta yi in za ta kwanta na safen ma ruwan alwala ya isar maka indai ta samu ruwan dimi ta kuskure bakinta wasu masu hikimarma domin hakorinsu ya yi karko suna daukar koren magani sabara su jika shi da gishiri su bar shi za su yi kuskurar baki da shi ba za su yi ‘Brush’ ba sai bayan sun ci abinci sannan su yi brush din sai kiga kin tsufa da hakoranki hakan yana kashe cututtuka baya kawo kansar hakori ko wasu cututtukan duk da ake samu to wasu ba za su kula zama ki iya samun alimmun ki dan digamar gishiri da ki jika shi ya kwana ki dauka ki yi dashi zuba ake yi a cika baki dashi a kuskura ya shiga ko ina ayi kamar sau uku sai ki ji hakori karkarkar ga aminci ga kwari.

Ana son mace ta iya yanga kallon miji kwarkasa yi mar tausa matsamar gabobi babu maganar an tsufa, data zauna kamshinta yana daukar hankalinsa ko fita ya yi babu wata mace da za ta dauke masa hankali domin a gidansa ya saba shi yasa zaki ga mace miji yana ofis ko kasuwa duk wani gwalangwa ana son mace baya birge shiba domin ya ga wanda yafi haka a gidansa.

Amma kiga wata a gidanta ita da kayan wanki ba a banbacesu rakwacan don haka da an zo an gilma ko ya jiyo kamshin turaren wata sai kiga ya yi sauri ya waiga sai kiga an tafi da hankalinsa, amma in kina gyarawa ya fi, nifa a kan miji don in yi masa gyara bana kasala.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Bana kuma yarda ba na tsufa ni har kullum gani nake daidai nake da zamanina saboda haka idan mace tana da miji kuma yana kan sha’awarta kada ta yadda ta tsufa koda kin shekara saba’in kin dan dana gyara ki yi kunshi ki yi ado ki yi masa kwalliya ki sa shi a gaba ba wani kayan fita unguwa ki yi adonki a gida miji ya gani ya yi sha’awar ki in kin yi kitso ko kunshi cire ki dan juya ya gani ko gyare kanki da sauran su dayawa, mata irin wannan yana kawo a samu ci gaba mai dinbin yawa a gidan aure.

Amma ta yaya aure da an yi wata uku wata ranka sai ya baci, kaya sun daka haka take jawosu bayan Allah ya ce, ‘TA’ARUFULLAH FIL RAKA WATA’ARUFU FISHSHIDDA’ Haka Manzon Allah Alaihissalatu Wassallam ya fada mana (Tara’arufullah raka kasan Allah cikin wadata da komai Wata’arufu fishshidda sai ya sanka yayin da tsanani ya zo maka) to an yi farkon auren ta dauki mai ta lafta dauki wannan ta lafta, lafce wannan lafce wancan ta dibi kaya ta zuba, wata kafin ta rufa wata biyar tasanye kayan lefenta kaf ina za a samu ko nutsuwa a ciki, abu babu tsari ba hankali ko kuma girki ta tittili mai dan kayan tallafin abokanen da aka dan kukkullo aka rako ango dashi da an yi baki, dauko taliya karya kaza zuba a dauko mai a sheka abin sam ba tsari, akwai lokacin da idan bako ya zo gidan ka ba zai ci abinci ba idan uku ta wuce a ka’ida bashi cikin abincin rana sai ki bashi ruwa da dan zobo wanda dama kin dafashi da dan kanunfari kin kukkulashi a leda bawani matsawa kai sai kun samu na kasar waje mai kyamikal kitafasa zobonki da kanunfari ki matsa lemon tsami ki zuba shi cikin kwalba baya komai inma baki da firij kisa a tukunya ki bar shi a rufe ki daure shi a leda ki zuba ruwa mai kyau da an yi baki ki dauko ki zuba dan sikarinki kadan ki gauraya ki basu shike nan ki cikasu da surutu maraba lale lale shike nan ba lallai sai kin dibi kayan abincin miji ki dafa musu ba amma idan kafin su zo sun fada miki shikenan sai ki fadawa maigidan cewar maigida yau zamu yi karin baki biyu shikenan sai ki dan kara abinci a yi kyakkyawar dahuwa ko ba nama ki samu tafarnuwa ki ka hada da kayan miyanki kika dan soyasu a mai kisa kayan kamshi sai sun soyu zaki ji gidan ya dumame da kamshi ki kawo ruwa ki zuba kiyi dafaduka mai kyau an takaita mata kayan miya mai ya fi fitowa sai kiga anci ana santi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Fasinjojin Farko Da Ba Sa Bukatar Bin Tsauraran Matakan Yaki Da COVID-19 Sun Sauka A Kasar Sin

Fasinjojin Farko Da Ba Sa Bukatar Bin Tsauraran Matakan Yaki Da COVID-19 Sun Sauka A Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

October 20, 2025
Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

October 20, 2025
Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

October 20, 2025
Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

October 20, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta

October 20, 2025
Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.