Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta kama wata matashiya, mai suna Maryam Haruna, mai shekaru 27 bisa zargin watsa wa wani matashi Lawan Inuwa Ibrahim, mai shekaru 25 tafasasshen ruwan shayi a jikinsa.
Kakakin ‘yansandan Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
- Ra’ayoyinku Kan Tasirin Amfani Da Kudi A Siyasar 2023
- ‘Yan Ta’adda Da Dama Sun Mutu A Wata Arangama Tsakanin ISWAP Da Boko Haram A Borno
ya ce, rundunar ta samu korafi ne daga wasu mutane a unguwar Rimin Auzinawa a ranar 11 ga watan Satumba, cewa wata mata ta kona Lawan Inuwa Ibrahim da ruwan shayi.
Haka kuma ya ce, “Bayan samun korafin ne rundunar ta tura jami’anta karkashin Baturen ‘yansanda na unguwar Rijiyar Zaki, CSP Usman Abdullahi, inda suka garzaya da matashin asibiti tare da cafke a wadda ake zargin”.
Kiyawa ya kara da cewa, “Bayan kai shi asibitin kwararru na Murtala Muhammad ne likitoci suka yi masa magani a fuska da hannunsa da kuma cikinsa da ya samu kuna tare da kwantar da shi a asibitin.
A nata bangaren, wadda aka cafke din ta amsa cewa ta watsa masa ruwan kuma ta yi hakan ne sakamakon rikici da ya varke a tsakaninsu.
A cewarta, tana zargin matashin da kashe mata aure ta hanyar kai tsurkunta wajen mijinta, inda ta kara da cewa shi matashin ne, lokacin su na kokawa, ya yi yunkurin watsa mata shayin.
Yanzu haka dai ana ci gaba da bincike kan lamarin.