Umm Hudaifa, matar shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi, na zaman gidan yari yanzu a Iraki, matar marigayi shugaban kungiyar Islamic State ta ba da labarin rayuwarta. Umm Hudaifa ce matar Abu Bakr al-Baghdadi ta farko kuma ta shaida lokacin da ya mulki bangarorin Syriya da Iraki a matsayin Daular Musulunci. Yanzu tana tsare a wani gidan yarin Iraki inda ake tuhumar ta da laifukan ta’addanci.
A bazarar shekarar 2014, Umm Hudaifa na zaune a Birnin Rakka, garin Syriya kenan da IS ta fi karfi a lokacin, tare da mijinta.
- Gwamnan Kano Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Kawo Karshen Fadan Daba A Kano
- Asibitin Yariman Bakura Ya Fara Amfana Da Dokar Ta-É“aci A Sashen Kiwon Lafiyar Zamfara
Yayin da jagoran da ake nema ruwa a jallo ke boye-boye a wurare daban-daban, a wannan lokacin ne ya tura dakaru su kwaso ‘ya’yanta biyu kanana. “Ya fada min cewa zai kai yaran ne don koya musu ninkaya a ruwa,” in ji Umma Hudaifa.
Akwai boyayyar talabijin da take amfani da ita a asirce.
Ina kunna ta idan ba ya gidan,” a cewarta ya zaci ba ta aiki. Ta kara da cewa an kebance ta daga sauran duniya ta hanyar hana ta amfani da duk wata na’ura kamar waya da kuma kallon talabijin tun daga shekarar 2007.
‘Yan kwanaki bayan daukar yaran, ta ce ta sha mamaki da ta kunna talabijin din ta ga mijinta na yi wa jama’a jawabi a babban masallacin al-Nuri da ke Birnin Mosul na Iraki ya na bayyana kansa karon farko a matsayin shugaban Daular Musulunci.
Yulin 2014
An ga bidiyon al-Baghdadi yana neman hadin kan Musulmai a matsayin shugabansu a duka fadin duniya sanye da bakaken kaya, wanda shi ne lokaci mafi girma a rayuwar kungiyar IS yayin da ta mamaye wasu yankunan Iraki da Syriya.
Umm Hudaifa ta ce ta kadu da gano cewa ‘ya’yanta suna Mosul tare da shi – ba wajen koyon ninkaya ba.
Mun samu wuri a wani dakin karatu inda muka yi magana tsawon awa biyu.
Yayin tattaunawar ta nuna cewa ita aka zalinta bayan ta yi yunkurin guduwa daga hannun mijin nata kuma ta musanta hannu a duk wasu ayyukan IS na rashin imani.
Hakan ya saba sosai da yadda aka bayyana ta a takardun kotu da aka shigar da karar da al’ummar Yazidi suka shigar, wadanda ‘yan IS suka yi garkuwa da su kuma suka yi musu fyade, sun zarge ta da hada baki wajen mayar da su bayi.
Ba ta daga kanta ba yayin hirar, ko sau daya. Tana sanye da bakaken kaya kuma wani bangare na fuskarta kawai ake gani, daga hancinta zuwa kasa.
An haifi Umm Hudaifa a 1976 a Iraki kuma ta auri Ibrahim Awad al-Badri, wanda daga baya aka sani da Abu Bakr al-Baghdadi a shekarar 1999.
Ya karanci fannin harkokin Shari’ar Musulunci a Jami’ar Baghdad kuma ta ce a lokacin yana da bin addini amma ba mai tsattsauran ra’ayi ba ne.
Sai kuma a 2004, shekara daya bayan Amurka ta jagoranci mamaye Iraki, dakarun Amurka suka tsare al-Baghdadi a sansanin Bucca da ke Kudancin kasar tare da wasu mazajen, wadanda daga baya suka zama jagororin IS.
Bayan sakinsa, ya yi ikirarin cewa ya sauya: “Ya koma mara fushi kuma ya daina yi wa mutane tsawa cikin fushi.”
Wasu da suka san shi sun ce ya fara hulda da al-Ka’ida ne kafin ya je sansanin Bucca, amma a cewarta daga wannan lokacin ne ya koma mai tsattsauran ra’ayi. “Ya fara samun matsala a tunaninsa,” in ji ta. Da aka tambaye ta dalili, sai ta ce “ya ga wasu abubuwa da ba za ku gane ba”.
Tana ganin duk da bai fada mata ba, amma “lokacin da ake tsare da shi an ci zarafinsa ta hanyar lalata”. Wasu hotuna da suka bulla na gidan yarin da Amurka ke jagoranta a Iraki mai suna Abu Ghraib sun nuna yadda ake tilasta wa fursunoni tayar wa da mutane sha’awa da kuma saka su yin wasu abubuwa na kaskanci.
Mun fada wa Ma’aikatar Tsaro ta Amurka zarge-zargen da ta yi amma ba ta ba da wata amsa ba.
Ta ce ta fara mamakin ko ya shiga wata kungiyar gwagwarmaya ne. “Na sha caje kayansa idan ya dawo gida, ko idan yana wanka ko kuma idan yana barci.
“Har jikinsa nake dubawa ko zan ga wani rauni, na yi mamaki,” a cewarta, amma ba ta ga komai ba.
“Na fada masa cewa, ‘Ka shiga hanyar bata, abin ya bata masa rai.”
Ta fadi yadda suke yawan sauya gidan zama, da yadda suka samu takardun bogi na karya, da yadda ya auri mace ta biyu. Umm Hudaifa ta ce ta nemi ya sake ta amma kuma ba za ta iya yarda da sharadin da ya ke gindaya mata ba, na cewar sai dai ta bar masa ‘ya’yanta, wanda hakan ya sa dole ta ci gaba da zama da shi a hakan.
Yayin da Iraki ta fada rikicin kungiyoyi da ya kai har 2008, ta san cewa lallai akwai hannunsa a bangaren kungiyoyin masu ikirarin jihadi na Sunni. A 2010 ya zama shugaban kungiyar Islamic State ta Iraki – bayan kafa ta a 2006, wata gamayya ce ta kungiyoyi masu ikirarin jihadi a Iraki.
“Mun koma Idlib a Syria a watan Janairun 2012, kuma a nan ne na fahimci cewa shi ne Khalifa,” in ji Umm Hudaifa.
Kungiyar Islamic State ta Iraki ta hade daga baya don kafa babbar Islamic State.
A lokacin, ta ce sai ya fara saka irin tufafin ‘yan Afghanistan, ya tara gemmu kuma ya fara daukar karamar bindiga.
Bayan lamarin tsaro ya tabarbare a Arewa maso Yammacin Syriya, sai suka koma Birnin Rakka, wanda daga baya IS ta mayar da shi babban birnin daularta.
Tuni aka san irin rashin imanin kungiyoyin da suka hadu suka zama IS, amma a 2014 da 2015 abin ya kara fitowa fili. Wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta gano cewa IS ta aikata kisan kare-dangi a kan al’ummar Yazidi marasa rinjaye.
IS kan yada rashin imaninta ta bidiyo. Ta kashe kusan mutum 1,700 wanda akasarinsu dakarun ‘yan Shi’a ne, yayin da suke dawowa daga wani sansani a Arewacin Bagadaza.
Sauran sun kunshi kona wani matukin jirgin sama dan kasar Jordan.
Wasu matan da suka zauna ‘yan IS yanzu na cewa ba su san yadda abin yake ba a lokacin, shi ya sa na matsa wa Umm Hudaifa kan ra’ayinta game da lokacin, ta ce ko a lokacin ba ta iya kallon hotunan rashin imanin saboda “zubar da jini haka kawai rashin imani ne kuma yin hakan keta alfarmar dan’adam ne”.
Umm Hudaifa ta ce ta kalubalanci mijinta game da “jinin mutanen da babu ruwansu” da ya zubar kuma ta fada masa “akwai abubuwan da za su iya yi kamar yadda Shari’ar Musuluncin ta tanada, kamar dora su kan hanyar tuba”.
Ta ce ya kan boye kwamfutarsa a cikin wata jaka. “Na yi kokarin shiga na ga abin da ke faruwa amma ba ni da ilimin kimiyya, kuma ko da yaushe kwamfutr sai ta tambaye ni kalmomin sirri.