Dubban al’umma ne suka fito zanga-zanga a Sakkwato tare da zagaya manyan tituna zuwa fadar Gwamnati rike da mabambantan kwalaye da ke nuna kasawar gwamnati wajen gudanar da mulki nagari.
Matasan wadanda suka gudanar da zanga-zangar ta lumana ba tare da wani tashin hankali ba sun rika rera wakokin bukatar gwamnati ta dawo da tallafin man fetur, bunkasa tsaro, inganta darajar naira da bude iyakokin kasa.
- Zanga-zanga: Gwamnati Ta Sanya Dokar Hana Zirga-zirga Ta Awa 24 A Kano
- Zanga-zanga: Kungiya Ta Gudanar Zanga-zangar Lumana A Jihar Filato
A cewarsu wadannan su ne manyan abubuwan da suka haifar da yunwa, talauci, haihuwar farashi da kuncin rayuwar da al’umma ke ciki.
Matasan sun yi mahada ne a gadar Alu a titin Kano tare da zagaya birnin a titunan Ali Akilu, Gawon Nama, Arkilla, Unguwar Rogo, Kanwuri, Ahmadu Bello, Gagi, Tamaje, Rawun Mai Ruwa, zuwa Fadar Gwamnati a inda jami’an tsaro suka hana masu shiga.
Jami’an tsaro a yanzu haka suna gudanar da sintiri a tituna a yayin da harkokin kasuwanci da ofisoshi suke ci-gaba da gudanar da ayyukan lafiya kalau. A yayin zanga-zangar wasu matasan sun lalata shingayen hanyar Ahmadu Bello, sai dai jagororin gangamin sun bukaci a hukunta wadanda suka yi barnar, sun kuma bayyana cewar tun farko sun bayyanawa jami’an tsaro hanyoyin da za su bi da kuna lokaci.