Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tana ci gaba da bincike kan dalilin da ya sa wata budurwa mai shekara 17 ta rataye kanta a kauyen Garin Dau da ke karmar hukumar Warawa a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa mafi akasarin mazauna kauyen sun zargi cewar budurwar ta rataye kan nata ne bisa auren dole da iyayenta ke shirin yi mata.
- Dole Ne Amurka Ta Dauki Alhakin Lalata Zaman Lafiya A Yankin Zirin Tekun Taiwan
- Ina Tausayin Wanda Zai Zama Shugaban Kasa, Saboda APC Ta Ruguza Nijeriya – Gumi
Sai dai iyayen nata sun musanta wannan zargi, inda suka ce ba ta kammala makarantar sakandare ba, balle a yi maganar aurar da ita.
Faruwar lamarim dai ya ya zo wa mazauna yankin da mamakin sakamakon yadda da dama daga cikin mutanen kauyen ke bayyana budurwar da kyawawan dabi’u.
Kwanaki biyu ke nan da rasuwar matashiyar mai shekaru 17 da ke aji biyu a makarantar sakandare, wadda aka tarar da gawarta a rataye kuma ana zargin ita ta rataye kanta.
Kakakin ‘yan sandan Kano, ya shaida cewar sun samu labarin faruwar lamarin, kuma suna bincike kan lamarin don gano shin budurwar ce ta rataye kan nata ko kuma akasin haka.
A shekarun baya dai an sha samun rahoton kashe kai da ‘yan mata ke yi kan auren dole.
Lamarin da ya sanya malamai suka shiga jan hankali da yin wa’azi ga iyaye da kuma su kansu ‘ya’yan kan matsalar da ke tattare da auren dole.