Matatar Dangote, ta fara fitar da mai daga matatar zuwa jasashen Afirka ta Yamma, a wani sabon yanayin kasuwanci da ka iya sauya kasuwar mai a Afirka.
Wani rahoto da mujallar Bloomberg ta fitar ranar Talata, inda ta ambato wasu bayanai da aka samu daga Vortexa da Kpler da Priecise Intelligence da ke bin diddigin bayanan jiragen ruwa, ya ce wani jirgin ruwa dauke da mai daga kamfanin Dangote, ya nufi kasar Togo.
- Xi Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Babban Taron Intanet Na Duniya Na Bana A Wuzhen
- Xi Jinping Ya Halarci Zaman Rufe Taron Kolin G20 A Rio De Janeiro
Rahoton, ya ce jirgi mai suna CL Jane Austen ya yi lodin mai sama da ganga 300,000 daga matatar Dangote.
A watan da ya gabata ne dai shugaban kamfanin man kasar Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ya ce kasar tana shirin sayen man daga hannun Dangote domin taimakon kasar wajen rage yawan kudaden da ta ke kashewa wajen shigar da mai daga nahiyar Turai kimanin dala 400 a kowane wata.