Matatar Man Fetur ta Dangote ta rage farashin man fetur daga Naira 850 zuwa Naira 820 kan kowace lita, wanda sabon farashin zai fara aiki daga ranar 12 ga watan Agusta, 2025.
Matatar ta ce wannan ragin farashi yana cikin jajircewarsa na tallafawa ci gaban ƙasa, tare da tabbatar da cewa an samu isasshen mai a ko da yaushe.
- ‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi
- Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo
Haka kuma, matatar ta sanar cewa daga ranar 15 ga watan Agusta, 2025, za ta fara amfani da sabbin manyan motoci 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG) wajen rarraba mai a duk faÉ—in Nijeriya.
Wannan mataki na zuwa ne, yayin da mutane suka fara ƙorafin farashin man fetur na ci gaba da tashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp