Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da matatar man Dangote a ranar 22 ga watan Mayun 2023, wanda ake fatan Nijeriya ta bunkasa karfin tace matatar man fetur a cikin gida da lita miliyan 103.34 a kowace rana.
Kamfanin Dangote ya bayyana ranar da za a kaddamar da matatun man da ake jira.
Matsalolin matatar mai a Nijeriya na tsawon shekaru za a magance su ne daga kamfanin matatar mai da man fetur na biliyoyin daloli.
A cewar wani rahoto da aka samu, aikin zai gudana ne a ranar 22 ga Mayu, 2023.
Yin amfani da wannan hanya na iya taimaka wa gwamnatin tarayya a kokarinta na dogaro da kanta wajen tace danyen mai a cikin gida domin daina kashe kudaden da ake amfani da su wajen shigo da mai.
Matatar Dangote, wadda ita ce matata daya mafi girma, za ta rika samar da ganga 650,000 a kowace rana, wanda hakan ke nufin jimillar man fetur da aka tace ya kai lita 103,341,742.
An ce an kamalla matatar man da gwaje-gwaje kafin kaddamar da aikin a halin yanzu.
Katafariyar matatar man Dangote da ke unguwar Lekki Free Zone a Jihar Legas, ta kai fadin kasa kimanin hekta 2,635, wanda ya fi girman tsibirin Victoria Island da ke Legas.
Kayayyakin aikin bututunsa shinne mafi girma a ko ina a duniya, yana da nisan kilomita 1,100 don sarrafa kafar Standard Cubic Feet na gas biliyan uku a kowace rana saboda yawan karfin matatar.
Rahotanni sun ce matatar ta na da tashar samar da wutar lantarki mai karfin MW 435 wanda ke iya bayar da jimillar wutar da kamfanin rarraba wutar lantarki ta Ibadan ke bukata.