Waiwaye Adon Tafiya, a yau zamu
Duba yadda wasu mata har yanzu wasu basu iya daurin dankwali ba:
Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa a wannan makon a cikin shirinmu na ado da kwalliya.
- Matatar Man Dangote Za Ta Fara Aiki A Ranar 22 Ga Watan Mayu
- Lardin Hunan Ya Samu Tagomashin Cinikayyar Waje Tsakanin Sa Da Kasashen Afirka A Rubu’in Farkon Bana
Yadda ake wannan daurin dankwali na ture kaga tsiya zaki dan shinfidashi sai ki dan ninka kadan haka sannan ki juya shi idan kina da abin da ake sawa saboda ya tsaya sai kisa shi kafin ki ninkashi, idan baki da shi zaki, iya amfani da takarda sai ki nunnunka ta dan tadanyi karfi haka sai ki dora kan dankwali dai dai inda zai zama a goshinki sai ki ninka shi ya dai dai fadin da ki keso sannan ki sake ninka shi za kiga yadda zai yi kyau ya tsaya kafin ki dora shi dama kin gyara gashinki saboda idan zaki yi ture kaga tsiya yafi kyau kanki a tsefe kin fake gashinki baya sannan kuma fakindin ya dan yi sama idan baki da gashi, sai ki dan samu wani abu wanda zai dan taimaka miki, sannan ki dakko wannan dankwalin da kika ninkashi sai ki dorashi saman girarki kadan haka amma karya yi sama so sai sai ki zagaya shi yabi tasaman kunnuwanki sai ki daureshi ta saman gashinki amma ba cokashi zaki yi ba daureshi zaki yi idan kika daure shi sai ki kama baki daya ki mike shi hannu ki guda biyu sannan ki yi ka kananan dashi harya kai jikin gashinki sai ki sassokeshi sannan ki kama dayamma kiyishi kamar yadda kika yi na farkon shima ki soke shi sannan ki juyu ta gaba kidan gyara zaki ga yadda kika yi kyau so sai.
Sannan bawai dole sai dogon dankwali ba zaki Iyayi da mai kwana hudu ma sai ki ninka shi kamar yadda zaki dauri gwaggwaro shima sai ki juyu tagaba ki ninkashi kamar yadda zaki wa dogon dan kwalin sannan ki juya shi kisa masa abun daurin dankwali ko kuma takardar idan kika masa haka sai ki yi kamar yadda kika daura mai dogon. Shima zakiga yadda ya hado.