Matsalar tasgadewar kashin baya, na faruwa musamman da kananan yara masu tasowa daga tsakanin shekara tara zuwa sha hudu, yayin da kasusuwansu suka fi jan gaba.
Wadanda ke gamuwa da wannan matsala, sun kai kamar kashi uku cikin 100 na kananan yara masu tasowa. Haka nan, matsalar ta fi faruwa ga ‘ya’ya mata, duk da cewa; wannan matsala na iya shafar kowa, sannan kuma a kowane irin shekaru.
- Jerin Tattaunawa Ta Musamman Da CMG Ya Gudanar Sun Maida Hankali Kan GGI
- A Karo Na Hudu ’Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Sun Yi Nasarar Kammala Ayyukansu A Wajen Kumbon
Haka zalika, wannan matsala na faruwa ne a yayin da wasu daga cikin jerin kasusuwan baya suka yi baka ko suka karkace zuwa hagu ko dama tare da murdewar jerin kasusuwan bayan.
Wannan baka ko karkacewa, na iya faruwa a ko’ina a jerin kasusuwan baya daga sama zuwa kasa. Wani yana yin sifar baka ko harafin ‘C’, ko kuma harafin ‘S’.
Sai dai, kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na wannan matsala, ba a san hakikanin dalilan faruwarta ba. Sai dai, matsalar ta fi yin kamari ga yara masu lalurar shan-inna, yaran da aka haifa da shanyewar kwakwalwa ko wadanda aka haifa da tawayar kashin gadon baya.
An raba nakasun bakan baya ko tasgadewar kashin bayan zuwa mataki uku a ma’aunin kusurwa na “Cobb angle”:
Mataki na farko: Mafi karancin nakasu (Cobb 10-25°)
Mataki na biyu: Matsakaicin nakasu (Cobb 26-40°)
Mataki na uku: Matsanancin nakasu (Cobb 50° zuwa sama).
A Mataki na daya da na biyu, likitan fisiyo na taimakawa wajen shawo kan matsalar da kuma magance ci gaban matsalar zuwa mataki na uku (Matsanancin nakasu), wanda sai ya bukaci yin aiki ko tiyata, domin gyara tasgadewar kashin bayan.
Matsalolin da ke tattare da tasgadewar kashin baya sun hada da:
1- Tawayar surar jiki
2- Matsalolin numfashi
3- Raguwar ingancin rayuwa da sauran makamantansu.
Haka nan kuma, matsalar na faruwa kadan da kadan ba tare da jin wani ciwo ba, sai dai; ana iya gamuwa da ciwon baya, ciwon kafada idan matsalar ta ta’azzara.
Ta yaya za a gane yaro ko yarinya na da wannan matsala?
Hanya mafi sauki da iyaye za su gane idan ‘ya’yansu suna da matsalar ta hada da sanya ido a gadon bayansu yayin sanya tufafi.
Abubuwan lura sun hada da cewa:
1- Kowace kafada ta yi saiti daidai ba tare da wata ta fi wata tudu ba.
2- Kowane allon kafada yana danfare da uwar jiki ba tare da daya ya bullo baya fiye da dayan ba.
3- Tsayin hannaye ya zamo bai-daya a yayin tsaiwa, ba tare da dya ya fi daya sauka kasa ba.
4- Gadon baya ya zamo bai-daya a yayin da aka durkusa (kamar yin ruku’u, amma tare da sakin hannaye zuwa kasa), ba tare da ganin wani doro a bangare daya na gadon baya ba, musamman a bangaren hakarkarin baya ko kasan allon kafada daya.
5- Gadon baya, ya zamo a mike yayin tsaiwa; ba tare da bayyanar siffar baka ko tasgadewa a tsakiyar gadon bayan ba.
Da zarar an lura da matsalar bakan baya, sai a yi maza a tuntubi likitan, domin magance matsalar tun da wuri kafin ta ta’azzara; har ta tilasta yin tiyatar baya, domin rike kasusuwan gadon baya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp