Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada bukatar amfani da manyan na’urorin zamani domin yaki da matsalar tsaro a Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki daya.
Gwamnan Jihar Zamfara da wasu gwamnonin jihohi sun gana da Amina J. Mohammed, Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya a birnin Washington D.C. ranar Juma’a.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Zamfara, Benuwai, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, da Neja.
Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina J. Mohammed ta yaba wa Gwamnonin kan kokarin da suke yi na ganin an magance matsalolin yankin.
“Kasancewar ku a nan ya nuna kwakkwarar sha’awar da Gwamnonin Arewa ke yi na aiwatar da sauyi a jihohinsu.
- Yadda Sojoji Suka Fatattaki ‘Yan Bindiga Tare Da Ceto Mutane 5 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
- Binciken Jin Ra’ayoyin Jama’a Na CGTN: Dokar Amurka Ta Ba Da Tallafin Kudi Ga Wasu Kasashe Ta Hargitsa Duniya
Da yake bayyana halin da ake ciki a Zamfara ga Mataimakiyar Babban Sakataren, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana muhimmiyar rawar da fasahar zamani za ta iya takawa wajen inganta tsaro da kuma bukatar hada karfi da karfe wajen amfani da karfin fasahar da ta hada da yin amfani da fasahar kere-kere, na’urorin tantance kwayoyin halitta da kyamarorin sa ido (CCTV).
“Muna nan da matsalolin da dama, amma babban kalubalenmu shi ne rashin tsaro, kuma dole ne a yi wani abu a kai.
“Saboda rashin tsaro, noma ya gagara. Muna bukatar taimako wajen bunkasa noma ta yadda za mu iya amfani fasaha wajen yaki da wannan tada kayar baya. Muna fatan samun mafita ga wadannan matsalolin yayin wadannan tarukan. Na karbi mulki a jiha mai cike da rashin aiki tare da karancin ci gaba.
“Na ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi da lafiya. Dole ne mu dauki matakin gaggawa don magance wadannan batutuwa masu muhimmanci; in ba haka ba, makomar mu za ta yi muni. Muna bukatar tallafi mai muhimmanci don shawo kan wadannan kalubalen da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga jama’armu.”