Biyo bayan kalubalen tsaro da ke addabar Jihohin Arewa da dama da kuma dadewar da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro suka yi wajen kawo karshen al’amarin, gwamnatocin jihohin yankin na yunkurin daukar nasu matakan, domin kawo karshen ta’addancin.
An bayar da rahotannin cewa, gwamnatocin jihohi da dama sun yi amfani da wadansu hanyoyi nasu na cikin gida, domin dakile yawaitar kashe-kashe, sace-sace jama’a da sauran matsalolin zaman lafiya da kuma barazana ga rayuwa.
Jihar Katsina, za ta sayi babura 700 da motoci kirar Hilus 20 da sauran makamantansu. Har ila yau, a jihar ta Katsina; gwamnati ta dauki matakan da suka dace, domin karfafa tsaro, musamman biyo bayan barkewar rashin tsaron a Karamar Hukumar Malumfashi.
Baya ga sayen motocin tsaro, gwamnatin kuma ta tabbatar da an tura jami’an tsaro a fadin jihar baki-daya.
Har ila yau, gwamnatin jihar ta Katsina ta amince da sayen baburan guda 700 ne da motoci kirar Hilus 20, a wani bangare na sabbin matakan dakile ayyukan ‘yan fashi da garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka a fadin jihar.
Kazalika, an amince da amincewar ne a taron majalisar zartarwa na jihar karo na 12, wanda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Katsina.
Da yake karin haske ga manema labarai bayan taron, kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ya ce, an sanar da matakin ne sakamakon mawuyacin halin da jihar ke ciki, wanda ya kawo babban kalubale ga ababen hawa na yau da kullum wajen shiga wasu yankunan, musamman na karkara da marasa galihu.
“Gwamnati ta bayyana matsayinta a fili: tsaro shi ne fifiko na farko, na biyu da na uku na wannan gwamnati shi ne, mun kudiri aniyar magance rashin tsaro baki-daya.” in ji Dakta Danmusa.
Baya ga motocin, majalisar ta kuma amince da sayo wasu kayan da suka hada da makaman yaki, na’urorin tsaro, kaki da sauran makamantansu.
Babu shakka, wadannan kayayyaki za su taimaka wa mutanen da ke kula da tsaron Jihar Katsina, wadanda za su hada kai da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da sauran jami’an tsaro.
Dakta Danmusa ya kuma bayyana cewa, majalisar ta kuma amince da sayen motoci kirar ‘Toyota Land Cruiser (Buffalo)’, guda takwas masu sulke, domin bunkasa zirga-zirga da kuma samar da tsaro a wuraren da ‘yan fashi ke addabar su.
“Wadannan matakan, wani bangare ne na kokarin da ake yin a karfafa tsare-taren tsaron al’umma da kuma samar da hukumomin hadakar tsaro kamar ‘yansanda, hukumomin tsaro na farin kaya (DSS) da jami’an ‘Cibil Difence’ da kuma sama musu kayayyakin aiki da suke bukata, domin yakar rashin tsaro yadda ya kamata,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da tallafa wa kokarin gwamnati, ta hanyar addu’o’i da bayar da hadin kai, sannan yana kuma mai tabbatar musu da aniyar gwamnati ta maido da dauwamamman zaman lafiya a fadin Jihar Katsina baki-daya.
Al’ummar Kurfi Sun Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya Da ‘Yan Bindiga A Katsina
A halin da ake ciki yanzu, shugabannin al’umma a Karamar Hukumar Kurfi da ke jihar, sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindigar da ke addabar yankin.
An dauki matakin ne, da nufin kawo karshen zubar da jini da sace-sacen shanu da kuma garkuwa da mutane da aka dauki tsawon shekaru ana yi.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, an yi sulhn ne mai cike da tarihi a ranar Alhamis cikin dajin Wurma, daya daga cikin wuraren da ake fama da rashin tsaro a yankin. Taron dai, ya gudane karkashin jagorancin Maradin Katsina, kuma Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi tare da shugaban karamar hukumar, Hon. Babangida Abdullahi Kurfi.
Da yake jawabi a wajen taron sulhun, Hakimin yankin ya bayyana wannan lokaci a matsayin wani lokaci na musamman ga al’ummar Kurfi,
“Wannan wani mataki ne na ci gaban al’ummarmu, domin kuwa mun zabi zaman lafiya, sannan kuma za mu kare wannan amana, saboda al’ummarmu,” in ji shi.
Har ila yau, ya bukaci shugabannin Fulani da su nada Sarakunan Gargajiya a tsakaninsu, domin karfafa rikon amana.
Manyan shugabannin Fulani da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga, Sani Muhindinge, Yahaya Sani (Wanda aka fi sani da Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu, sun yi alkawarin kawo karshen kashe-kashe, garkuwa da mutane da sace-sacen shanu.
Sun bayar da tabbacin cewa, yanzu manoma za su iya komawa gonakinsu, ba tare da wata fargaba ba.
Jihar Borno
Hadin kai tsakanin Gwamnatin Jihar Borno da hukumomin tsaro, ya bayar da gudunmawa kwarai da gaske ga zaman lafiyar da aka samu a jihar sama da shekara 14 na rikicin Boko Haram.
Gwamna Babagana Umara Zulum, ya ci gaba da rokon gwamnatin tarayya da ta kara tura sojoji, yayin da kuma ya bai wa jami’an tsaro motocin sintiri sama 300 da kuma Babura sama 500.
Kirkirar kungiyar CJTF, wato kungiyar sa kai ta matasa, ta taimaka wa kokarin sojoji tare da rage yawan kai hare-hare.
Gwamnan, ya kuma bayar da gudunmawar gidaje tare da bayar da gudunmawar kudi ga sojojin da suka jikkata da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
Kwara Ta Dauki Dakarun Tsaron Gandun Daji
A yunkurinta na fatattakar masu aikata laifuka, Gwamnatin Jihar Kwara ta kwararrun ‘yan banga a matsayin jami’an tsaron gandun daji.
Domin tabbatar da zirga-zirgarsu, jihar da kananan hukuomi 16, sun sayi Babura 320 don amfani da su a dazuka, musamman kuma a wurare masu wahala.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazak, ya kuma gudanar da taron tuntuba da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a yankin Kwara ta Arewa da kuma Kudu, kan ayyuka da dabarun jami’an tsaro.
Kaduna Ta Yi Amfani Da Tattaunawa Da Kuma Karfin Soja
Gwamnatin Jihar Kaduna, ta Uba Sani ta yi amfani da tattaunawa da kuma karfin soja, domin dakile matsalar rashin tsaro.
A cewar Kwamishinan Yada Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, kungiyar tattaunawa ta zaman lafiya ta Kaduna, ta kasance jigo wajen dawo da tubabbun ‘yan ta’adda.
Ya yi magana ne a taron bude kasuwar dabbobi ta Kara a Birnini Gwari, wadda aka rufe sama da shekara 10, sakamakon matsalar tsaro.
“Dabarunmu, su ne na ganin mun aiwatar da ingantattun ayyuka tare da karfafa tattalin arzikin al’umma da ci gaban matasa da kuma hadin kan shugabanninmu na gargajiya,” in ji Maiyaki.
Har ila yau, ya kara da cewa; an kwato sama da hekta 500,000 na filaye, sakamakon samun zaman lafiya da aka yi.
Yobe Ta Gudanar Da Bincike Kan Matsalar Tsaro
A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni; ya kaddamar da wani shiri na duba lamarin tsaro, biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a Kananan Hukumomin Gaidam, Gujba da kuma Yunusari.
Birgediya Janar Abdulsalam Dahiru mai ritaya, mai ba da shawara ta musamman kan harkokin tsaro ya ce, kutsawa daga yankunan da ke makwabtaka da su ne ya haddasa tashe-tashen hankula na baya-bayan nan.
Har ila yau, ya tabbatar da cewa; an samu kwanciyar hankali, sakamakon yadda jami’an tsaro suka jajirce ta hanyar daukar matakan da suka dace.
Kusancin da ke tsakanin Yobe da Borno da kuma Jamhuriyar Nijar ce tasa matsalar tsaro ta ta’azzara.
Sansanin Sojoji Da Aka Kafa A Birnin Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya dauki batun kashe-kashe das ace-sacen mutane zuwa ga manyan hafsoshin tsaro, lamarin day a sa aka amince da kafa sansanin soji a shiyyar da ke fama da rikicin.
Daraktan tsaro, Abdulrahman Zagga, ya ce; hafsoshin tsaro da jiragen sama da na ruwa, sun ziyarci jihar tare da bayar da gudunmawar yadda za a shawo kan lamarin.
Ya yi nuni da cewa, taron masu ruwa da tsaki; wanda ya kunshi ‘yan banga da sauran shugabannin al’umma, ya yi matukar rage matsalar rashin tsaro.
Gwamnatin Sakkwato Ta Taimaka Wa Jami’an Tsaro
Gwamnatin Jihar Sakkwato, karkashin Gwamna Ahmed Aliyu, ta bayar da tallafi ga jami’an tsaro.
Baya ga kayan aiki da kuma tallafi, gwamnatin ta bullo da sabbin dabaru tare da yin kira da a tallafa wa jama’a, domin yaki da aikata laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp