A makonnin da suka gabata ne, ministan kudi da kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed ta bayar da sanarwar cewa gwamnatin tarayya tana tunanin samun naira tiriliyan 8.5 a shekara ta 2023.
Idan muka yi la’akari da yanayin barayin mai da rashin tsaro da matsalolin tattalin arzikin duniya, za a iya cewa wannan hasashe na tattalin arziki ba daidai ba ne.
Muna fatan ‘yan majalisa za su mayar da hankalinsu sosai wajen duba wannan lamari na hasashe.
Duk da cewa mafi yawansu ba za su dawo kujerarsu ba, kenan wannan ne damarsu ta karshe. Ya kamata su yi abin da za a yaba masu ko za a rika tuna su a tarihi mai kyau.
Gwamnatin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta watanni kadan ne ya rage mata kafin ta hannata wa sabuwar gwamnatin da ta sami nasara a zaben 2023. Batun gaskiya ba za a iya gane ainihin yanayin tattalin arzikin Nijeriya ba har sai bayan wannan gwamnatin da muke ciki a halin yanzu ta shude.
Haka kuma, ministan ta fitar da daftarin cewa za a kashe naira tiriliyan 19.8, wanda shi ne ma kasafin kudi mafi yawa a tarihin Nijeriya.
Bayanai na nuna cewa gwamnati na bukatar bashin naira tiriliyan 11.3 don cike gibin kasafin kudi na shekara ta 2023. Wannan makudan kudade shi ne babban abun damuwar da kowa ya kamata hankalinsa ya koma kai.
A gaba daya gwamnati na samun kudaden kasafin kudinta na shekara daga kudaden shigarta ne. wadanda suka hada da haraji da sauran kasuwancin da gwamnati take yi kamar sayar da danyen mai na Nijeriya.
Kasashe da suke samun rara a kasafin kudinsu su ne wadanda suke kashe kudadensu kasa da kudaden shigarsu. Lokaci na karshe da Nijeriya ta sami rara a akasafin kudinta shi ne 2003, 2004 da 2005.
A duk lokacin da kudaden shiga suka gaza, kasa za ta iya nemo bashi don ta yi abubuwan da suka wajaba a kanta.
A batun gaskiya ‘yan kasa ba sa son gwamnatinsu ta rika karbo bashi ba dubawa. Ba wai hujja ba ne a ce kasashe irin su Amurka ko Japan ko Germany ko Butaniya suna amso bashi. Abun damuwar ita ce mutane da dama sun fahimci cewa gwamnati ba ta yin abubuwan da suka dace da kudaden da take amsowa.
A halin da ake ciki yanzu haka, Nijeriya tana kashe dukkanin kudaden shigarta a wajen biyan bashi ne, kuma matsalar ga al’umma ba a san yaushe za a warware wannan matsalar bashin ba. Mutane suna son su rika kwatanta bashin kasa da kasa kamar bashin wata kungiya ko magidanta.
Abun fa ba haka ba ne. Kasashe ba kasuwanci daya suke yi ba a tsakaninsu, kowacce kasa tana da kudadenta da dokokinta da yadda take karbar haraji da yadda take gudanar da harkokin kasuwancinta.
A zahiri matsalar kudade kasa ba zai iya kasancewa ana da isasshen kudaden da za su iya ba, amma kasa za ta iya warware matsalar bashinta saboda matsalolli da ka iya tasowa ba tare da isassun kudade ba, kamar abun da muka gani a Rasha kwanan nan.
Yanayin tattalin da kuma daidaitonsa ba za a iya biyan bashin da ake bin Nijeriya ba har sai an bi wadansu dokoki biyu, wanda ga bayaninsu ta yadda kowa ma zai iya fahimtarsu duk da yake ba kai-tsaye suke ba.
Na farko, kaddara cewa kudaden da ake sa ran samu suna daidai da bashin da ake bi, sai dauki kudin ruwa kai-tsaye zuwa asusun ajiya. A hasashen kudin da kasa ta yi ba za a iya biyan bashin da ake bin ta ba da wuri.
Na biyu, kasar a yanayin da take ciki na tattalin arziki ba za ta iya karbo bashi ta biya bashi da shi ba. Dokar kamar tsarin nan na Stopcok da ke cikin Ponzi Game. Ponzi game yananayi ne da kasa za ta karbo bashi ta biya wadanda ta karbo bashi a wurinsu. Bashin da ake karba kullum karuwa suke yi saboda kudin ruwan da suke cikinsu.
A bisa yanayin kididdigan da ake da su, bashin da ake bin Nijeriya da ke karuwa duk shekara a shekarar 2022 ya kai akalla kashi 4 cikin 100 kasa da yadda aka aro a shekarar 2021.
A maimakon kasar ta aro sama da kashi 40 wajen kashe kudade a shekarar 2022. Hakan na nuna cewa gwamnati ta ari naira 4 a kowacce naira 10 na kudaden shigar da ake samu, kuma ma har yanzu shekarar ba ta kare ba.
A saboda haka al’ummar kasa suna da damar da za su rika nuna damuwarsu kan yadda basussukan da ake bin Nijeriya ke kara hauhawa saboda babu wani shiri da zai iya saukar da wannan bashin da ake bin kasa.
Wajibi ne ‘yan majalisa su duba da idon basira don ganin sun tabbatar ana bin dokoki yadda suka dace ba. Wajibi ne majalisun kasa su sake duba dokokin yadda ake kashe kudade da kuma na babban bankin Nijeriya (CBN) tare da sanya doka da hukunta duk wanda ya karya doka, a kuma tabbata da samun mutanen da suka dace a kan kowani mukami.
Amma fa wannan ga shugabannin majalisar dattawa da wakiali masu zuwa, domin wadannan an zo bakin kofa.
Dakta Nasir Aminu
Dr. Nasir Aminu, Malami ne a Jami’ar Cardiff Metropolitan University da ke Birtaniya