Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwarsa dangane da matsalolin da kasar nan ke fama da su a halin yanzu.
Ya ce Nijeriya tana fama da matsaloli masu tarin yawa da suka zarce na 2015 lokacin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amshi mulki a hannun tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
- Ganduje Zai Sanya Hannu Kan Takardar Kashe Malamin Nan Da Ya Kashe Daliba Hanifa — Gwamnatin Kano
- ‘Yar Shekara 11 Mai Baiwar Lissafi A Kano Ta Samu Tallafin Karatu Na Bankin Duniya
Sanusi wanda ke magana a Legas a wajen wani taron biki da raba kyautuka na gidauniyar Akinjide Adeosun (AAF).
“Wannan kasa ce mai dumbin arzikin tattalin Mai a daidai lokacin da farashin arzikin Mai ya yi tashin gauron zabi sakamakon yakin kasar Russia da Ukraine.
Kudaden shigarmu ba za su iya biyan basukan da ke kanmu ba. Kuma idan wani bai fahimci muna cikin matsala ba, to muna ciki.
“Muna cikin ramin matsala a 2015. Daga 2015 zuwa yanzu kuma mun kara zulmiya cikin ramin matsala.
“Tabbas mun fuskanci babbar matsala a 2015 amma idan aka kwatanta 2015 da yanzu ba wani sauyi illa ma matsalolin da suka karu,”
“Muna ta fama da matsalolin ‘yan ta’adda, hauhawar farashin kayayyaki, ga matsalar hauhawar farashin kudaden canji, kuma abun damuwar ma shi ne masu mulkin suna tunanin zamu jijjina musu da yaba musu idan sun bar ofis, to dai babu wani canjin da aka samu.” Cewar Sanusi Lamido.