Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa Ƙarƙashin Jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta lura da halin da Kano ke ciki domin ya shafi martabar masarautu a ƙasar Hausa.
Cikin wata sanarwa a rubuce da jaridar Daily Trust ta wallafa, majalisar ta yi kira ga dukkanin ɓangarorin biyu da su tabbatar da gudanuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma rahotanni sun bayyana cewa guda daga ciki ya garzaya kotu don haka yanzu magana na ƙarƙashin shari’a.
- Malaman Kano Sun Roki Tinubu Ya Bari A Yi Sulhu Kan Rikicin Masarautar Jihar
- Ina Nan A Matsayin Sarkin Kano, Har Sai Na Ga Umarnin Kotun – Sanusi II
Sanarwar na ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin gudanarwa mai martaba Lawal Hassan Gummi OFR, Sarkin Gummi. Shugaban Kwamitin Gudanarwa na majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa (NTRC).
Majalisar ta yi addu’ar Allah ya ƙaro zaman lafiya a Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp