Sabon Ministan harkokin Gidaje da raya Birane, Yusuf Ata, ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC idan har aka ci gaba da riƙe Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar Kano.
Ata, wanda aka rantsar a matsayin minista a ranar 4 ga Nuwamba, ya bayyana hakan ne yayin taron APC na ƙaramar hukumar Fagge a Kano, gabanin taron NEC da NWC na jam’iyyar da za a gudanar a Abuja.
Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano ya ce rashin adalci da halayen shugabannin jam’iyyar ne suka haddasa rashin nasarar APC a zaɓen 2023. Ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da shan kaye idan har ba a sauya shugabancinta ba. Ata ya jaddada cewa APC za ta sake fuskantar faɗuwa idan aka bar shugabannin jam’iyyar na yanzu su ci gaba da jan ragama.
- Tabbas Sin Za Ta Ci Gaba Da Jan Zarenta A 2025
- Ganduje Ya Haifar Da Babbar Matsala Ga Ci Gaban Al’ummar Kano – Gwamna Abba
Ata ya ce ba za su lamunci shugabancin da bai dace da su ba, yana mai cewa suna da cikakken imani cewa ikon Allah ne ke bayar da mulki, ba ƙuri’u ko kuɗi ba. Ya ce sun yi imani cewa Nasiru Gawuna da Yusuf Garo ne suka lashe zaɓen 2023, amma an tafka maguɗi, kuma kotu ta tabbatar da hakan.
Ya bayyana cewa idan APC ta ci gaba da riƙe shugabanni irinsu Abbas, to zai fice daga jam’iyyar, yana mai cewa hakan na iya haifar da sake faɗuwa a gaba. Abdullahi Abbas dai yana kan wa’adinsa na uku a matsayin shugaban APC a Kano.