Babban Bankin Duniya ya ce, muddin Nijeriya ta gaza farkawa domin gyara tsarin tara harajinta da kuma mayar da hankali akan wasu bangarorin domin bunkasa kudaden shigartar ba, to kudaden shigarta za su ci gaba da raguwa wanda hakan kuma babban barazana ce da ka iya ruguza cigabanta.
Punch ta nakalto ce wani babban jami’i a Babban Bankin Duniyar, Mr Rajul Awasthi ne ya bayyana haka a wani taro akan muhimmanci yi wa tsarin haraji kwaskwarima domin cigaban kasa, wacce wata kungiyarsa ido kan tattalin arzikin Nijeriya ta shirya.
Ya ce akwai bukatar Nijeriya ya cire Bada tallafin mai gaba daya, yana mai cewa duk da cewa farashin man fetur na laruwa a kasuwannin duniya, Nijeriya ba ta samu cin gajiyar wannan dama ba saboda makudan kudaden da take kashewa akan rarar man fetur.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa batun cire tallafin Mai dai shine batu da ke yawo a kasar a halin yanzu inda wasu masana ke ganin cire tallafin zai taimaka wa cigaban tattalin arzikin kasar a yayin da wasu kuma ke ganin hakan ba cigaba ba ne domin kuwa zai Kai farashin Man ya yi tsada da abubuwan masarufi za su yi tashin gauron zabi a kasuwa, don haka ne suke kira da cewa kada a cire tallafin.
Ita kuma Gwamnatin tarayya ta ce jire tallafin zai Bada damar narka rarar kudin da za ta samu sakamakon cirewar zuwa wasu sassan inganta rayuwar jama’a kuma za su samu karin kudaden shiga ta hanyar man.