Gwamnatin jihar Kano ta sauya ranar da za a koma makarantun firamare da Sakandire a jihar zuwa ranar Talata 17 ga Satumba 2024.
Amma dalibai a makarantun kwana a fadin jihar za su koma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.
- Zaben Kananan Hukumomi: A Magance Maimaita Magudi A Jihar Kaduna
- Ya Kamata A Magance Shigar Banza A Masana’antar Kannywood -Samha M Inuwa
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce, kwamishinan ilimi na jihar, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa, sauyin ya biyo bayan ayyana ranar 16 ga watan Satumban 2024 a matsayin ranar hutu domin bikin Mauludin Annabi Muhammad (SAW).
”An sauya ranar komawa kananan makarantu a fadin jihar ne don bai wa dalibai damar gudanar da bukukuwan wannan rana mai alfarma da ke nuna ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).
“A yayin da nake taya al’ummar Musulmi murna, ina kira gare su da su rungumi dabi’ar hakuri, sadaukarwa, da kishin kasa, su ci gaba da yi wa jihar da kasa baki daya addu’a,” inji shi.