Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, 2022 a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar haihuwar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW).
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar zagayowar ranar ta bana.
- 2023: Jam’iyyu 18 Ne Za Su Yi Takarar Gwamna A Jihohi 28, ‘Yan Takara 10,231 Ke Neman Kujerar Majalisar Dokoki —INEC
- Yara 3 Sun Tsere Daga Maboyar ‘Yan Bindiga Yayin Da Suke Barci A Abuja
Aregbesola, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar, Dakta Shu’aib Belgore, ya gargadi daukacin ‘yan Nijeriya da su kasance masu nuna soyayya, hakuri, juriya da kyawawan dabi’u irin wadanda Manzon Allah (SAW) ya koyar.
A cewarsa hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.
Aregbesola ya bukaci ‘yan Nkjeriya musamman musulmi da su guji tashin hankali da rashin bin doka da oda da sauran ayyukan laifuka.
Ya ce, “Dole ne mu nuna shugabanci na gari a Afirka.”
Yayin da yake kira da a dakatar da duk wata dabi’a ta raba kan al’umma a fadin kasar nan, ya bukaci daukacin ‘yan Nijeriya musamman matasa da su rungumi dabi’ar aiki tukuru da zaman lafiya da ‘yan’uwansu, ba tare da la’akari da bambamcin addini, akida, zamantakewa da kabilanci ba.
Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su kasance masu lura da sha’anin tsaro, inda ya bukaci su kai rahoton wadanda suke zargi ko wani abu ga hukumar tsaro mafi kusa ko kuma ta hanyar aike da sakon kar ta kwana ta wayoyin da ama tanadar.