Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya dawo Nijeriya bayan ziyartar Ingila.
Tinubu, wanda ya bar kasar a ranar 24 ga watan Satumba, ya dawo a ranar Alhamis.
- Yara 3 Sun Tsere Daga Maboyar ‘Yan Bindiga Yayin Da Suke Barci A Abuja
- Dan Bindiga Ya Kashe Kananan Yara ‘Yan Makaranta 36 A Thailand
Lokaci na karshe da ya halarci wani taron jama’a tun ranar 22 ga Satumba, lokacin da ya gana da mambobin kungiyar bishop a Abuja.
A lokacin da ya tafi, an yi ta nuna damuwa game da inda shiga, musamman bayan da ya kasa rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben 2023.
Sai dai, Kashim Shettima, abokin takarar Tinubu ne ya wakilce shi a wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a cibiyar taron kasa da kasa (ICC) da ke Abuja.
Daga baya hotunansa sun bayyana a kafafen sada zumunta inda suka nuna shi a Birtaniya.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, tsohon gwamnan Jihar Legas ya ziyarci Faransa da Birtaniya.
Leadership Hausa ta rawaito cewa Tinubu zai isa kasar ne ranar Alhamis gabanin wani muhimmin taro a Abuja ranar Juma’a.
“Zai dawo kafin karshen mako,” kamar yadda wata majiya ta bayyana.