Rundunar dakarun hadin gwiwa ta kasashe hudu da ke yaki da Boko Haram (MNJTF) da ke Ndjamena na kasar Chadi ta bayar da rahoton yadda yan ta’adda ke ci gaba da mika wuya.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, Laftanal Kanar Abubakar Abdullahi, ta ce cikin wadanda suka ajiye makamansu dun hada da wasu matasa biyu da aka bayyana su a matsayin kwararru a kwance abubuwan fashewa.
- Yanzu-Yanzu: Jami’an Tsaro Sun Cafke Jami’in Binance A Kenya
- Sojoji Sun Lalata Masana’antar Sarrafa Burodin ‘Yan Ta’adda A Borno
Abubakar Mohammed mai shekaru 19 da Bana Modu dan shekaru 13, sun mika wuya a garin Munguno a ranar 21 ga watan Afrilu.
Lamarin ya zama nasara a yakin da sojoji ke yi na murkushe mayakan Boko Haram a yankin.
Cikin kayayyakin da aka gano a wurinsu akwai abubuwan fashewa biyu da wayoyin hannu biyu da kudi Naira 53,000.
Rundunar ta bayyana kwarin gwiwarta kan yakin da ta ke yi da mayakan na Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya da wasu kasashe da ke da iyaka da kasar.