Majalisar dinkin duniya na shirin sake shirya taron gaggawa don duba yiwuwar kada kuri’ar amincewa da tsagaita wuta a Gaza, matakin da ke zuwa daidai lokacin da rashin abinci ke galabaitar da jama’ar yankin.
Wannan sabon yunkuri na zuwa ne a daidai lokacin da fararen hula ke dada rasa rayuka sanadin ruwan wutar da Isra’ila ke yi a sassan yankin.
- ECOWAS Ta Shimfida Sabbin Ka’idoji Domin Janye Wa Nijar Takunkumi
- Kuri’ar Kin Amincewar Amurka Ta Tsagaita Wuta A Gaza Adawa Ce Ga Bukatar Bil’adama
Ko a makon da ya gabata sai da majalisar dinkin duniya ta gudanar da makamancin taron, amma Amurka ta hau kujerar naki kan tayin tsagaita wuta a Gaza, lamarin da ya sa aka tashi taron ba tare da cimma matsaya ba.
A yayin jawabin da suka gabatar, wakilan tawagar kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a ziyarar da suka kai mashigin Rafaa na iyakar Masar, sun tabbatar da irin tashin hankalin da al’ummar Gaza ke ciki, kasancewar babu wani tudun mun tsira yanzu haka a yankin.
Ko da yake amsa tambayar manema labarai, wakilin kasar China a tawagar Zhang Jun ya ce tura ta kai bango, lokaci ya yi da ya kamata a tsagaita wuta haka.
Kusan dukannin kasashe mambobin majalisar dinkin duniya sun goyi bayan tsagaita wuta, in ban da Amurka da ke ganin har yanzu Isra’ila na daukar Fansa kan harin da Hamas ta kai kasar watanni biyu da suka gabata.