A ranar Lahadi, 15 ga watan Disamban 2024 ne kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, ta amince da ficewar kasashen Sahel wato Nijar, Mali da Burkina Faso daga kungiyar.
Kungiyar ta bayar da sanarwar ne a karshen taron koli da ta yi a Abuja, Babban Birnin Nijeriya, inda ta ce daga ranar 29 ga watan Janairun shekara mai kamawa kasashen uku za su daina zama mambobin kungiyar.
- Babban Aikin “Samar Da Lantarki Daga Hasken Rana A Wajen Da Ake Kiwon Kifi” A Sin Ya Fara Aiki
- Gwamnatin Katsina Ta Sha Alwashin Dakile Rikici Tsakanin Makiyaya Da Manoma
A farkon shekarar nan ne kasashen uku suka fitar da sanarwar hadin gwiwa ta bukatar ficewa, saboda a cewarsu kungiyar ta kasa magance matsalolin tsaro na kungiyoyi masu ikirarin jihadi da ke da alaka da ISIS da al-Kaeda da ke neman wargaza yankin.
Me ya sa ECOWAS ta amince?
BBC ta yi tattauna dakta El Haroon Muhammad, masani a harkar diflomasiyya da dabarun raya kasashe, ya ce dole ce ta sa Ecowas daukar matakin saboda babu alama cewa wadannan kasashen za su dawo cikin kungiyar.
”Yadda suka rungumi kasar Rasha, yadda suke mu’amala da Turkiyya da Iran, suka kawo musu tsare-tsare da zai kawo ci gaban kasashen da bunkasar tattalin arzikinsu, dole ne ECOWAS ta dubi wannan matsayin” a cewar shi.
A taron da kungiyar ta yi ranar lahadi, ta kuma ce kofa a bude take ga kasashen Sahel din nan da watanni shida idan sun sauya shawara suna so su koma cikin kungiyar.
Dakta El Haroon ya ce sake ba su damar ba zai yi amfani ba saboda kasashen na duba amfanin kansu ne.
“Abin da zai kara lalata al’amarin shi ne yadda shugaban Nijeriya ya zama babban aminin Faransa, wanda ya ce hakan zai kara firgita kasashen su janye jikinsu.”
Wace irin riba ficewar kasashen Sahel ukun zai yi ga ECOWAS?
Dakta El Haroon Muhammad ya ce babu wata riba da kungiyar ECOWAS za ta ci, illa ta kara faduwa.
”Idan aka dauki tarihin kungiyar ta ECOWAS, yau wajen shekara 40, duk abubuwan da ta sa a gaba za ta yi ba ta yi su ba, idan tafiya ta kama dan mamban kasar zai je makwabciyar kasar, irin wahalar da zai sha a hannun jami’an tsaro, kwastam da sojoji sai ya yi wayyo Allah.”
Ya kuma ce kasashen kungiyar sun kasa yin kudin kansu, sun kasa inganta kasuwanci, manufarsu na kawo habakar tattalin arziki da magance talauci duk sun gaza.
Wace irin riba kasashe ukun za su ci bayan ficewarsu?
Masanin harkar diflomasiyyar da dabarun raya kasashe Dakta Elharoon Muhammad ya ce janye jikin kasashen uku daga kungiyar shi ne alheri a gare su kuma akwai riba da yawa wadanda sun ma fara ganin wasu daga ciki.
”Ga riba nan suna ci, irin tatsar arzikin da Faransa ta yi musu, ta rike musu wuya, da suka kori Faransa ga shi nan suna ta walwala da su na bunkasa suna kuma fadada harkokinsu da kasashen waje. Su ke cin riba,” inj i Dakta El-Haroon.
Ya kuma ce dole ne kasashen sun yi haka saboda sun dade kasar Faransa na bautar da su, suna daga cikin kasashen da su ka fi koma baya a duniya, kuma yin haka shi ne mafi alheri a gare su.
”Tsakanin lokacin da kasashen suka kai ruwa rana da Faransa zuwa yanzu an ga sauye-sauyen da suka faru a kasashen.”